Damagum: Shugaban PDP Ya Fadi Dalilin Kin Hukunta Masu Kawo Cikas a Jam'iyyar
- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Amb. Umar Iliyasu Damagum, ya yi magana kan rikicin da jam'iyyar ke fama da shi
- Umar Damagum ya bayyana cewa lokacin da ya hau kujerar shugancin jam'iyyar, ya same ta cikin tarin matsaloli
- Shugaban na PDP ya nuna akwai masu ganin laifinsa kan kin daukar matakin ladabtarwa kan wasu mambobin jam'iyyar da suka saba doka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, ya yi tsokaci kan kin daukar matakin ladabtarwa kan wasu mambobin jam'iyyar.
Umar Damagum ya bayyana cewa ya ki amincewa da matsin lamba don hukunta wasu mambobin PDP da suka yi kuskure ne domin kare muradun jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Damagum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin taron kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya yanke hukuncin yin sulhu ne kan batun ladabtar da wasu mambobi ne saboda maslahar jam’iyyar baki ɗaya.
Shugaban PDP ya yaba da hukuncin kotu
Sai dai ya tabbatar cewa duk da matsalolin shari’a da suka taso a farko, babban taron PDP na kasa na 2025 zai gudana kamar yadda aka tsara.
Ya kuma bukaci sabon kwamitin gudanarwa na (NWC) da za a zaba ya kunshi mutanen kirki, masu gaskiya da amana, waɗanda za su iya farfaɗo da jam'iyyar daga tushe.
“Jiya, 4 ga Nuwamba 2025, mai shari’a Akintola ya yanke hukunci mai tarihi wanda ya tabbatar cewa jam’iyyarmu ta cika dukkan sharuddan doka, don haka tana da cikakken ikon gudanar da harkokinta na dimokuraɗiyya ciki har da gudanar da taron 2025."
“Dole na bayyana cewa abin da mai shari’a Akintola ya yi a wannan lokacin na tsoratarwa da shisshigin siyasa ga bangaren shari'a, abin jarumta ne."
“A wannan lokaci da ake barazana ga bangaren shari'a, ya zabi yin karfin hali wajen tsayawa da gaskiya da kare doka. Wannan hukunci nasara ce ba kawai ga PDP ba, har ma ga dimokuraɗiyya gaba ɗaya."
- Umar Damagum
Meyasa ba a yi hukunci ba?
Damagum ya tuna cewa lokacin da ya hau kujerar mukaddashin shugaban PDP, ya tarar da jam’iyyar cike da rarrabuwar kai da rashin jituwa tsakanin ɓangarori.

Source: Twitter
“Na gane cewa abin da jam’iyyarmu ke bukata a lokacin ba ramuwar gayya ba ce, ba fushi ba ne, ba zargi ba ne, sulhu take bukata. Dole ne mu magance matsalolin da aka samu bayan zaben 2023."
“A lokacin, wasu sun yi tunanin cewa ina goyon bayan wani ɓangare ne saboda na ki sanya kaina cikin ramuwar gayya kan wadanda suke so a hukunta. Amma na san abin da nake yi."
“Da suka kasa fahimtar hikimar hakan, sai suka bar jam’iyyar. Amma har yanzu, wadanda ake zargin ina tare da su sun kasa gane niyyata."
"Gaskiya ita ce duk wani mataki da na dauka, duk wani sulhu da na yi, don jam’iyya na yi, ba don mutum ko kungiya ba."

Kara karanta wannan
Tsagin Wike ya mamaye sakatariyar PDP, an samu mukaddashin shugaban jam'iyya na kasa
- Umar Damagum
An dakatar da Damagum a PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagin PDP mai biyayya ga Nyesom Wike, ya sanar da dakatar da Umar Damagum daga shugabancin jam'iyyar.
Sun bayyana cewa an dakatar da Damagum ne saboda zargin rashin iya jagoranci da sama da fadi da kudaden jam'iyyar.
Hakazalika an kuma dakatar da wasu karin mambobin kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

