"Bai da Wani Zabi": Wike Ya Gano Dalilin Atiku Na Ficewa daga Jam'iyyar PDP
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sake taso da batun ficewar Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP watanni bayan aukuwar hakan
- Nyesom Wike ya bayyana cewa dole kanwar na ki ce ta sanya tsohon mataimakin shugaban kasar ya tattara 'yan komatsansa ya fice daga PDP
- Hakazalika, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya zargi masu sauya sheka daga PDP da cewa su ne suka lalata jam'iyyar kafin su fice
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake taso da batun ficewar Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP.
Nyesom Wike ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, bai da wani zaɓi illa barin jam’iyyar PDP.

Source: Facebook
Nyesom Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Tsagin Wike ya mamaye sakatariyar PDP, an samu mukaddashin shugaban jam'iyya na kasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar ya fice daga PDP
Idan ba a manta ba dai a ranar 14 ga watan Yulin 2025, Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
A lokacin Atiku ya bayyana cewa jam’iyyar ta kauce daga ainihin manufofinta kuma ta yi nisa cikin rikice-rikicen da ba za a iya warwarewa ba.
Me Nyesom Wike ya ce kan Atiku?
A yayin hirar, Wike ya bayyana cewa ficewar Atiku daga jam’iyyar adawa da abin da ya zama dole, saboda ya kasa amfani da PDP don cimma burinsa na siyasa.
“Atiku bai da wani zaɓi illa barin PDP, saboda yana son amfani da jam’iyyar don burinsa, amma yana sane cewa idan ina nan, ba zai samu damar yin hakan ba."
- Nyesom Wike
Wike ya kuma zargi tsohon mataimakin shugaban kasar da sauran waɗanda suka sauya sheka da cewa sun lalata jam’iyyar PDP.
“Waɗannan su ne mutanen da suka lalata jam’iyyar. Sau nawa Atiku ya bar PDP kuma ya dawo?”
- Nyesom Wike
Wike ya soki gwamnan jihar Bayelsa
Ministan ya kuma caccaki Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, wanda ya koma jam’iyyar APC a hukumance a ranar Litinin.

Source: Facebook
“Diri ya ce ya bar PDP, kuma ni ina ɗaya daga cikin mutanen da suka fi farin ciki a yau."
“Shi da Makinde sun ce ba za su bari wani ya lalata PDP ba. To yanzu wa gari ya waya."
- Nyesom Wike
Wike ya zargi Gwamna Diri da munafurci yana mai cewa a baya shi ne ke kiran wasu ‘yan jam’iyya a matsayin ‘masu shirin birne PDP’, amma yanzu shi ya koma APC.
Wike ya fasa kwai kan rikicin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana mutanen da ke da laifi wajen ruguza jam'iyyar PDP.
Nyesom Wike ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu murus saboda abin da ya kira rashin bin tsarin dimokuradiyya da dokokin da suka kafa ta.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi
Ministan ya zargi gwamnonin PDP da wasa da makomar jam’iyyar, yana mai cewa irin yadda suke tafiyar da jam’iyyar, zai kai ta ga rugujewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
