Tsagin Wike Ya Mamaye Sakatariyar PDP, An Samu Mukaddashin Shugaban Jam'iyya na Kasa

Tsagin Wike Ya Mamaye Sakatariyar PDP, An Samu Mukaddashin Shugaban Jam'iyya na Kasa

  • Sabon mukaddashin shugaban PDP na kasa, Abdulrahman Mohammed ya kama aiki a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja yau Litinin
  • Mohammed, wanda kwamitin NWC da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya nada, ya ce burinsa dawo da martabar PDP
  • Ya sha alwashin cewa zai kawo karshen rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP tare da shirya babban taro na kasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza yayin da tsagin Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya karbi ragamar jagorancin jam'iyyar.

Mataimakin shugaban PDP na kasa (Arewa ta Tsakiya), Abdulrahman Mohammed ya kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar yayin da rikici ya kara zafi.

Sanata Samuel Anyanwu.
Hoton Sanata Samuel Anyanwu da wasu mambobin NWC da ke goyon bayansa Hoto: @SamuelAnyanwu
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne bayan kwamitin gudanarwa (NWC) wanda sakataren PDP, Sanata Samuel Anyanwu ke jagoranta ya dakatar da Umar Damagum.

Kara karanta wannan

Rikici ya tsananta: Zanga zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed ya karbi ragamar PDP

Bayan ya isa sakatariyar PDP da ke Abuja, Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa an nada shi a matsayin shugaban jam'iyyar na riko.

"Yau mun dauki nauyin dawo da zaman lafiya da daidaito a PDP. Kowa ya san jam'iyyar mu ta al'umma ceba ta mutum daya ba," in ji shi.

A wani taro da aka gudanar a ƙaramin ofishin PDP da ke Wuse, Abuja, Mohammed ya yi jawabi kan manufarsa, inda ya nuna damuwarsa kan halin da jam’iyyar ta tsinci kanta a ciki.

“Kowa ya san irin halin da jam’iyyarmu ta fada saboda ayyukan wasu shugabanni da mambobi. A baya mun kwawhe shekaru 16 jam'iyyar PDP na mulki ba tare da katsewa ba.
"Amma yanzu shekaru fiye da goma muna cikin adawa, muna fama da ficewar gwamnoni, ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi."

- Abdulrahman Mohammed.

Manufar shugaban PDP na tsagin Wike

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Bayan PDP ta dare 2, kallo ya koma kan iko da hedkwatar jam'iyyar

Mohammed ya ce ya karɓi wannan mukami ne “saboda haka Allah ya kaddaro da kuma goyon bayan manyan jiga-jigai a cikin jam’iyya."

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce sake farfado da tsarin PDP da dawo da zaman lafiya da dimokuraɗiyya a cikin gida, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

"A matsayina na Mukaddashin Shugaban PDP, burina shi ne warkar da raunukan jam’iyyar mu da kawo ƙarshen rabuwar kai,” in ji Mohammed.
Umar Damagum.
Hoton wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na PDP (NWC) a wurin taro a Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Ya yi alkawarin sake farfado da PDP ta hanyar gudanar da babban taron kasa na hadin kai da kammala zabukan da ba a yi ba daga matakin jihohi har zuwa kananan hukumomi da mazabu.

Dalilin Gwamna Diri na barin PDP

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya ce ya dauki matakin barin PDP ne saboda maslahar al'ummar jiharsa amma ba kowa zai fahimta ba.

Gwamna Diri ya ce siyasa hanya ce da mutum zai yi wa jama'a hidima kuma ya ba da gudummawa wajen samar da ci gaba, dom haka bai kamata yan siyasa su kullaci juna ba.

Kara karanta wannan

"Nan gaba za ku gode mini," Gwamma Diri ya fadi asalin dalilin ficewarsa daga PDP

A watan da ya gabata ne Gwamna Diri ya sanar da ficewarsa daga PDP, kuma ana sa ran zai koma jam'iyyar APC a hukumance ranar Litinin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262