Rikici Ya Tsananta: Zanga Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyyar PDP da ke Abuja

Rikici Ya Tsananta: Zanga Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyyar PDP da ke Abuja

  • Rigimar shugabanci tsakanin tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike da bangaren Umar Damagum ya kara tsananta a PDP
  • Magoya bayan sabon mukaddashin shugaba da bangaren Wike ya nada, Abdulrahman Mohammed sun barke da zanga-zanga
  • Sun bukaci Ambasada Damagum da duk mambobin NWC da ke goyon bayansa, su bar sakatariyar jam'iyyar PDP nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Zanga-zanga ta barke a babbar sakatariyar jam'iyyar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja yau Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.

Wasu mambobin PDP sun barke da zanga-zanga ne domin nuna goyon bayansu ga tsagin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Mohammed Abdulrahman.

Kara karanta wannan

Tsagin Wike ya mamaye sakatariyar PDP, an samu mukaddashin shugaban jam'iyya na kasa

Masu zanga zanga.
Hoton yadda magoya bayan tsagin Wike suka barke da zanga-zanga da na shugaban PDP, Umar Damagum Hoto: @Nigeriainformation, @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa masu zanga-zangar, wadanda rera wakokin goyon baya, sun bukaci kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da Umar Damagum ke jagoranta ya bar ofishin nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin PDP ya kara tsananta

Rahotanni sun nuna cewa an naɗa Abdulrahman Mohammed a matsayin mukaddashin shugaban PDP a makon da ya gabata, bayan rikicin shugabanci ya kara tsananta.

Tsagin da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda sakataren PDP, Sanata Samuel Anyanwu ke jagoranta ne ya nada Mohammed, wanda shi ne mataimakin shugaba (Arewa ta Tsakiya).

Tun farko dai PDP karkashin jagorancin Damagum ta dakatar da Sanata Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade, mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, na tsawon wata guda.

A daya bangaren, tsagin jam’iyyar da ke biyayya ga Wike, ya gudanar da wani taro a wani wuri daban a Abuja, inda suka ayyana dakatar da kwamitin Damagum gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Bayan PDP ta dare 2, kallo ya koma kan iko da hedkwatar jam'iyyar

Masu zanga-zanga sun fadi bukatarsu

Masu zanga-zangar sun zargi Damagum da rashin gaskiya da karkatar da harkokin jam’iyya, suna masu rantsuwa cewa za su kwace ikon sakatariyar domin tabbatar da Mohammed Abdulrahman.

Leadership ta ce an tura jami’an tsaro zuwa wurin don hana barkewar rikici yayin da bangarorin biyu ke takaddama kan ikon mallakar sakatariyar PDP da ke Abuja.

Sanata Samuel Anyanwu.
Hoton sakataren PDP na kasa kuma jagoran magoya bayan tsagin Wike, Sanata Samuel Anyanwu Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka bangaren Mohammed Abdulrahman sun karɓi iko da ofishin shugaban jam’iyya na kasa.

Da yake magana da manema labarai a ofishinsa, Abdulrahman ya ce zai haɗa kan mambobi tare da farfado da jam’iyyar domin shiryawa babban zaben gaba.

“Mun kuduri aniyar yin aiki don ci gaban jam’iyyarmu mai daraja. Za mu hada kai mu dawo da mutuncin PDP kamar yadda take a da,” in ji shi.

PDP ta yi fatali da hukuncin kotu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta bayyana aniyarta na gudanar da babban taronta na kasa kamar yadda ta tsara duk da hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

Masana'antar Kannywood ta yi babban rashi, Allah ya karbi ran Malam Nata'ala

Tun farko, kotun tarayya mai zama a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da taron bayan zargin cewa jam’iyyar ta karya dokokinta na cikin gida.

Amma jam'iyyar PDP ta yi fatali da wannan hukunci, tana mai umartar mambobinta su ci gaba shirin babban taro kamar yadda aka tsara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262