Ana Wata ga Wata: Bayan PDP Ta Dare 2, Kallo Ya Koma kan Iko da Hedkwatar Jam'iyyar

Ana Wata ga Wata: Bayan PDP Ta Dare 2, Kallo Ya Koma kan Iko da Hedkwatar Jam'iyyar

  • Kallo ya koma sama kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP wanda ya jawo aka samu bangarori biyu masu hamayya da juna
  • Dukkanin bangarorin biyu na shirin karbe iko da hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja domin ci gaba da gudanar da harkokin siyasa
  • Wannan matakin ya jefa fargaba da zaman dar-dar a tsakanin ma'aikatan da ke aiki a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rikicin PDP ya dauki sabon salo bayan da aka samu bangarori biyu masu hamayya da juna na Umar Damagum, shugaban jam’iyyar na kasa, da na Sanata Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na kasa.

Dukkanin bangarorin biyu na shirin komawa aiki yau a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza, a birnin Abuja.

Jam'iyyar PDP ta sake shiga rikici
Sakataren PDP na kasa, Samuel Anyanwu da shugaban jam'iyyar, Umar Iliya Damagum Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska
Source: Facebook

Jam'iyyar PDP ta rabu gida 2

Kara karanta wannan

Rikici ya tsananta: Zanga zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja

Majiyoyi masu tushe sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa dukkan bangarorin biyu sun shirya komawa yin aiki a hedikwatar jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin bangarorin dai ya jawo tsananin fargaba a tsakanin ma’aikata.

A ranar Asabar, bangaren Damagum da ’yan kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) sun gudanar da taro a Legacy House da ke Maitama, Abuja.

Hakazalika bangaren Anyanwu ya gudanar da wani taron daban a ofishinsa da ke Wuse.

Bangarorin PDP na shirin yin tarurruka

Wata majiya daga jam'iyyar ta bayyana cewa dukkanin bangarorin biyu sun shirya gudanar da tarurruka a hedkwatar PDP ta kasa.

“Abin da muke ji shi ne bangaren Anyanwu ma yana son yin taro a hedkwatar jam’iyyar gobe (wato yau). Tun bayan hukuncin kotu a ranar Juma’a, dukkan bangarorin biyu suna ta gudanar da tarurruka don kammala dabarun su."
"Idan su duka suka zo Wadata Plaza, bangaren Anyanwu da na Damagum, ba mu san abin da zai faru ba. Ma’aikata suna cikin fargaba sosai."
“Bangaren Wike na kokarin jawo wasu mambobin NWC zuwa gefensu. Suna neman karin yawan mutane ne, idan suka fi ɗayan bangaren yawa, komai zai iya faruwa.”

Kara karanta wannan

Matasan APC sun bukaci gwamnan Sokoto ya nemi tazarce, an ji dalili

- Wata majiya

Jam'iyyar PDP ta samu kanta cikin rikici
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP za ta yi babban taronta na kasa

Wata majiyar cikin gida kuma ya tabbatar da cewa duk da hukuncin kotu, bangaren Damagum tare da gwamnonin PDP suna da niyyar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa.

An dai tsara gudanar da babban taron ne a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, a birnin Ibadan, jihar Oyo.

Kotu ta dakatar da babban taron PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta kawo cikas ga shirin jam'iyyar PDP na gudanar da babban taronta na kasa.

Kotun da ke karkashin jagorancin mai shari'a, James Omotosho, ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa, wanda ta shirya yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Hakan na zuwa ne bayan wasu masu shigar da kara da ake zargin magoya bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ne sun bukaci kotu ta hana gudanar da taron.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng