Gwamnan Taraba Ya Dauki Mataki na Sauya Sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC

Gwamnan Taraba Ya Dauki Mataki na Sauya Sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC

  • Ana hasashen Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba zai sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan tattaunawa da jama’a
  • Yanzu haka dai jam'iyyar APC a jihar Taraba ta bayyana cewa ta shirya karbar gwamnan da dukkanin mukarrabansa
  • Matakin na Kefar na zuwa ne bayan sauya shekar wasu gwamnonin PDP kamar Peter Mbah da Sheriff Oborevwori

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Siyasar jihar Taraba na shirin daukar sabon salo yayin da ake hasashen Gwamna Agbu Kefas zai iya sauya sheka daga PDP zuwa APC a kowane lokaci.

Kefa na iya zama na gaba daga cikin gwamnonin jam’iyyar PDP da za su sauya sheka zuwa APC, bayan da takwaransa na Enugu, Peter Mbah, ya koma a ranar Talata.

Ana hasashen cewa gwamnan Taraba, Kefas Agbu zai koma jam'iyyar APC daga PDP
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas zaune a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Jalingo. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Gwamna ya kafa kwamitin sauya sheka

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya sake tabo batun sulhu da 'yan bindiga a Katsina

A cewar majiyoyin jaridar Daily Trust, Gwamna Kefas ya kafa kwamiti karkashin jagorancin tsohon Sanata Dahiru Bako, kan sauya shekarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce kwamitin ne zai gudanar da tattaunawa da manyan ‘yan siyasa da jama’ar gari kafin gwamnan ya yanke hukunci kan matakin da zai dauka.

A yayin daya daga cikin tarukan, Sanata Bako ya ce:

“Gwamnan ba zai dauki irin wannan mataki ba tare da jin ra’ayin jama’a da neman shawararsu ba. Shi ya sa muke gudanar da wadannan tarurruka."

APC ta shirya karbar gwamnan Taraba

A ranar Talata, matasa a Jalingo suka gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka yi kira ga gwamnan da ya sauya sheka zuwa APC. Wannan ya sa ake tunanin zai iya daukar mataki nan kusa.

APC a Taraba ta riga ta bayyana shirinta na karbar gwamnan tare da mukarrabansa, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka ce hakan zai karfafa jam’iyyar a yankin Arewa maso Gabas.

Sai dai wasu cikin ‘yan jam’iyyar APC na nuna fargaba cewa idan Kefas ya sauya sheka tare da ‘yan majalisar jiha da kwamishinonin PDP, hakan zai iya dakile su a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tauraruwar Kano ta kara haskawa, jihar ta samu babban nasara a sauyin yanayi

An ce gwamnan Taraba ya kafa kwamitin tuntuba domin shirya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya jagoranci taron majalisar zartarwa (SEC) a Jalingo. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Taraba: PDP ta yi martani kan jita-jitar

An yi kokarin jin ta bakin manyan hadiman gwamnan – Emmanuel Bello (mai ba da shawara kan yada labarai) da Josiah Kente (mai ba da shawara kan harkokin siyasa) – amma basu amsa kira ba.

Sai dai shugaban PDP na jiha, Alhaji Abubakar Bawa, ya karyata zancen, yana cewa, “wannan gangami na APC ne kawai,” kuma ya ki yin tsokaci kan ayyukan kwamitin da aka kafa.

Rahotanni na cewa matakin Kefas na zuwa ne bayan da gwamnonin Enugu (Peter Mbah), Delta (Sheriff Oborevwori) da Akwa Ibom (Umo Eno) suka bar PDP a bana, abin da ya kara raunin jam’iyyar a jihohin da ta daɗe tana mulki tun daga 1999.

APC ta dawo iko da jihohi 24 a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC mai mullki a kasa, yanzu tana da iko da jihohin Najeriya 24 bayan sauya shekar gwamnan Enugu, Peter Mbah.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya kalli gwamna ido da ido, ya caccake shi a zaman makoki

A ranar Talata muka rahoto cewa Peter Mbah ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC, inda ya ce hakan zai sanya jihar Enugu ta samu ci gaba mai yawa.

Sauya shekar Peter Mbah ya sa APC ta kara yawan jihohohin da take mulki daga 23 zuwa 24, yayin da PDP ke da jihohi takwas kacal, bayan murabus din gwamnan Bayelsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com