Malamin Addini Ya Kalli Gwamna Ido da Ido, Ya Caccake Shi a Zaman Makoki

Malamin Addini Ya Kalli Gwamna Ido da Ido, Ya Caccake Shi a Zaman Makoki

  • Babban limamin coci a Kwara, Fasto Israel Amoo, ya soki Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a yayin jana’izar tsohon gwamna
  • Wasu daga cikin mahalarta jana’izar sun yi tafi da goyon baya ga limamin, yayin da wasu suka ce bai dace ya yi irin wannan magana ba
  • Iyalin marigayi tsohon gwamna sun nesanta kansu daga kalaman limamin kiristan, suna mai cewa ba su san da abin da zai faɗa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara — Maganganu sun biyo bayan sukar da Fasto Israel Amoo ya yi wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara.

Babban limamin cocin a Kwara ya caccaki gwamnan yayin huduba a jana’izar tsohon gwamnan jihar, Cornelius Olatunji Adebayo.

An fadawa gwamnan Kwara gaskkya kan mulki a zaman makoki
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara a yayin taro. Hoto: Kwara State Government.
Source: Twitter

Fasto ya fadawa gwamna gaskiya a zaman makoki

Rahoton TheCable ya ce jana’izar ta gudana ne a Cocin 'All Saints Anglican', Oke-Onigbin, a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Edo: Gwamna ya dauki mataki mai tsauri, ya kori kwamishina daga aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin jawabinsa, Fasto Amoo ya zargi gwamnatin jihar Kwara da rashin kula da tsofaffin ma’aikata da rashin biyan kudin ritaya da fansho.

Sannan ya koka game da mummunan halin da hanyoyin yankin Kwara ta Kudu suke ciki, yana cewa hakan na kawo cikas ga yaki da rashin tsaro.

Ya ce:

“Hanyar zuwa wannan gari abin tsoro ce. Na tabbata kuma kun bi wannan hanya, kuma kun ga yadda ta lalace.
“Ta zama matsala wajen yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane. Ta yaya jami’an tsaro za su kai dauki da gaggawa daga Ilorin idan hanyoyin haka suke?”

Ya kuma tunatar da gwamnan cewa duk wata rayuwa tana da iyaka, yana cewa ya kamata yadda ake rayuwa a yau ya zama abin da za a tuna da shi bayan mutuwa.

Wadannan kalamai sun jawo ce-ce-ku-ce daga jama’ar da suka halarci jana’izar, wasu sun yaba masa, yayin da wasu suka ce bai dace limamin ya yi irin wannan magana a jana’iza ba.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Bayan taron, magoya bayan Gwamna AbdulRazaq sun fito sun soki wa’azin limamin, suna cewa yana da nufin siyasa kuma an yi hakan ne don tozarta gwamnan a bainar jama’a.

Iyalan marigayi sun yi magana bayan Fasto ya soki gwamna
Tsohon gwamnan jihar Kwara da ya rasu, Cornelius Adebayo. Hoto: Aproko Kwara.
Source: Facebook

Martanin iyalan marigayin tsohon Gwamna a Kwara

A cikin wata sanarwa da ‘yar sa ta fari, Bukunola Ajayi ta fitar, dangin tsohon gwamnan sun nesanta kansu daga kalaman limamin.

Sun tabbatar da cewa ba su san da abin da zai faɗa ba kuma ba su zabe shi don ya yi jawabi a wurin jana’izar ba, cewar rahoton Daily Post.

Iyalan sun kara da cewa kalaman limamin ba su da alaka da dangin Adebayo, kuma ba su san da abin da zai yi ba kafin jana’izar.

“Mahaifinmu mutum ne mai son zaman lafiya da girmama hukuma. Abin takaici ne cewa jana’izarsa ta zama wurin da aka yi amfani da dama wajen yin kalamai marasa dadi.
“Muna ba da haƙuri idan wannan ya haifar da damuwa ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, kuma muna godiya bisa goyon bayan da ya bai wa iyalanmu yayin jana’izar."

- Cewar sanarwar

An fara bikin birne tsohon gwamnan Kwara

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP a Enugu ya sauya sheka, ya hade da Tinubu a APC

A baya, kun ji cewa an fara shirye-shiryen jana’izar tsohon gwamnan Kwara wanda ya rasu a birnin Abuja yana da shekara 84 a duniya.

Hidimomin za su hada da daren tunawa da shi a Abuja da kuma jana’iza a cocin All Saints a Oke Onigbin da ke jihar Kwara.

Cornelius Olatunji Adebayo.ya taba zama gwamna, sanata, minista, da mamba a hukumar NADECO.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.