Ta Faru Ta Kare, Kotu Ta Yi Hukunci kan Halascin Takarar Jonathan a Zaben 2027
- An samu sabon hukunci kan cancantar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shiga takarar zaben shugaban kasa a 2027
- Wata kotu a Yenagoa ta yanke hukuncin bayan da wasu 'yan jam'iyyar APC suka shigar da kara kan hana Jonathan yin takara
- Mai shari'a Mai shari’a Isa H. Dashen ya bayyana cewa Jonathan na da 'yancin takara, kuma ya yi bayani kan sashe 137(3)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yenagoa - Rigimar da ake yi kan cancantar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shiga takarar zaben shugaban kasa na 2027 ta dauki sabon salo a makon da ya gabata.
A makon jiya ne, aka ruwaito cewa wata kotu ta cire duk wani shinge da ake ganin zai iya kange rantsar da Jonathan a karo na uku a matsayin shugaban kasa.

Source: Twitter
An je kotu don hana Jonathan yin takara
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, wasu masu adawa da takarar Jonathan sun ce ba zai yiwu a sake rantsar da shi sau uku ba, sabo da sashi na 137(3) na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan sashe ya yi tanadin cewa babu wani mutum da aka zaba a mukamin gwamnati a Najeriya da za a iya rantsar da shi fiye da sau biyu.
Suna kuma yin hakan ne bisa ga rantsar da tsohon shugaban kasar a 2010 bayan mutuwar magabacinsa, marigayi shugaba Umaru 'Yar'Adua, da kuma 2011 lokacin da ya lashe zabensa.
Jonathan ya bar ofis a shekarar 2015 bayan ya fadi zabe, kuma sashin na 137(3) bai zama doka ba sai a 2018, shekaru uku bayan saukarsa daga mulki.
Kotu ta ba Jonathan damar yin takara
Mun ruwaito cewa, wasu shugabannin jam’iyyar PDP na zawarcin Jonathan a kan ya zo ya tsaya takarar zaben shugaban kasa na 2027 a inuwar jam’iyyar.
Domin duba yiwuwar ko Jonathan na da 'yancin sake yin takara, wata kotun tarayya da ke a Yenagoa, ta saurari karar wasu 'yan APC.
Alkalin kotun, Mai shari’a Isa H. Dashen, ya yi dogon zance a kan takardar da Jonathan ya gabatar don kare kansa a lokacin da yake nazarin rahotannin da aka gabatar a ranar 27 ga Mayu, 2022.
Mai shari’a Isa H. Dashen ya ce ba za a iya hana Jonathan yin takara a zaben shugaban kasa a nan gaba ba bisa sashi na 137(3) na kundin tsarin mulki.

Source: UGC
INEC, APC sun ki halartar zaman kotu
Jaridar Arise News ta ruwaito cewa Mai shari’a Dashen ya amince da matsayin tsohon shugaban kasar, na cancantar tsaya wa takara.
An ce jam’iyyar APC da hukumar INEC, wadanda aka hada su a matsayin wadanda ake kara a shari'ar da wasu mutane biyu, Andy Solomon da Ibidiye Abraham ('yan APC), suka shigar, sun gaza halartar kotun duk da an mika musu takardar gayyata.
Hakan ya tilasta wa alkalin kotun bayyana cewa, kin halartarsu, ya nuna cewa sun amince da duk bayanan da suka shafi karar da masu shigar da karar da Jonathan suka yi.
Joanthan ya tuno cin amanar 'yan siyasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa ya fadi zaben 2015 ne saboda cin amanar wasu 'yan siyasar Najeriya.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon shugaban ma’aikatan fadarsa, Mike Oghiadomhe.
Goodluck Jonathan ya kuma yi bayanin halayen 'yan siyasar Najeriya, musamman na rashin gaskiya da kuma saurin cin amanar mutum.
Asali: Legit.ng


