A Hankali APC Na Rasa Jiga-Jiganta, Ana Jita-Jitan Sanatan Sakkwato Zai Koma ADC

A Hankali APC Na Rasa Jiga-Jiganta, Ana Jita-Jitan Sanatan Sakkwato Zai Koma ADC

  • Majiya ta bayyana yiwuwar sanatan Sakkwato ya bar APC ya koma sabuwar jam’iyyar gamayya ta ADC da ke tashe a yanzu
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka kafa wata tafiyar ‘yan siyasar Najeriya da ke burin kifar da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu
  • Ba wannan ne karon farko da ake kafa jam’iyyar siyasa ba don kawar da wata gwamnati a Najeriya, APC ma a haka ta fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Sakkwato - Jita-jita mai ƙarfi na yawo a fagen siyasar jihar Sakkwato cewa Sanata Ibrahim Lamiɗo, wanda ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin barin jam’iyyar APC domin komawa sabuwar jam’iyya mai suna ADC kafin babban zaɓen 2027.

Wannan jita-jita ta fara karfi ne bayan wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga jihohi daban-daban suka fara kafa tubalin jam’iyyar ADC da nufin ƙarfafa gwiwar ‘yan adawa domin kayar da APC mai mulki a babban zaɓen da ke tafe.

Ana jita-jita sanatan Sakkwato zai bar APC
An fara hango sanata a ADC: Senator Ibrahim Lamido
Asali: Facebook

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Sanata Lamiɗo ba ya mu’amala da gwamnatin APC a jihar Sakkwato, inda aka lura cewa dangantakarsa ta fi karkata ga wasu ‘yan adawa fiye da jagororin APC a matakin jiha.

Sanata ya daina hulda da ‘yan APC

Wani ɗan siyasa daga cikin jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa Aminiya cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sama da shekara ɗaya ba mu ga Sanata Lamiɗo a taron gwamnati ko na APC ba. Don haka ba za mu yi mamakin ficewarsa ba.”

Shi kuwa Kabiru Wurno, daya daga cikin magoya bayan APC, ya ce akwai yiwuwar Sanatan ya sauya sheƙa.

A cewarsa:

“Lamiɗo yana son sake tsayawa takara a 2027, amma da wuya APC ta ba shi dama saboda ba ya tare da manyan jagororinta. Dole ya nemi wata hanya.”

Magoya bayan sanata sun yi Imani da hukuncinsa

Sanata zai iya barin APC
Sanata Ibrahim Lamiɗo na Dab da Barin APC, Zai Koma ADC?: Senator Ibrahim Lamido
Asali: Facebook

A wata jiha daban, wasu magoya bayan Sanatan sun bayyana goyon bayansu gare shi muddin ya fice daga jam’iyyar. Shu’aibu Muhammad daga Sabon Birni ya ce:

“Da zai shirya da Wamakko, da za su yi ƙarfi tare. Siyasar Gabas tana buƙatar haɗin kai.”

Ya’u Muhammad daga Goronyo kuwa ya ce:

“Idan har Sanata Lamiɗo zai fice daga APC, muna tare da shi. Shi mutum ne da ke tallafa wa matasa da marasa galihu.”

Babu batun barin APC a hukumance

Sai dai wani makusancin Sanatan ya bayyana cewa ba zai bayyana komai a yanzu ba, yana mai cewa Sanatan da kansa zai bayyana matsayinsa a lokacin da ya dace.

Ko da yake Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sanata Ibrahim Lamiɗo don jin sahihancin labarin, amma ba a samu nasara ba.

Yanzu haka, al’ummar Sakkwato da dama na dakon ganin matakin da Sanata Lamiɗo zai ɗauka, musamman kafin babban taron jam’iyyar ADC da ake sa ran gudanarwa a cikin ‘yan makonnin nan.

Wani rikicin APC a Sakkwato

A wani labarin na daban, tun 2024 rikicin jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya dauki sabon salo tsakanin manyan jihar.

Duk da nasarar da jam'iyyar ta samu a jihar daga PDP, hakan ya zamo mata kalubale da take fama da shi.

Leadership ta ce an yi ta kokarin rufa-rufa kan rigimar jam'iyyar amma yanayin sai kara fitowa yake daga 'ya'yanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.