Ana Ta Shirin 2023, Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Sokoto Sun Koma APC

Ana Ta Shirin 2023, Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Sokoto Sun Koma APC

  • Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Sokoto sun bayyana barin jam'iyyar tare da bayyana komawa APC
  • Sun ce sun rasa kwarin gwiwar ci gaba da zama a PDP, kuma ba sa ganin jam'iyyar za ta yi nasara a zaben mai zuwa
  • Jam'iyyar APC da PDP na ci gaba da samun musayar mambobi yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa

Jihar Sokoto - Wasu jiga-jigai kuma masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun bayyana sauya sheka a jihar Sokoto zuwa jam'iyya mai ci ta APC, The Nation ta ruwaito.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, jam'iyyun APC da PDP na ci gaba da fuskantar kaura a 'yan kwanakin nan yayin da ake tunkarar zaben 2023.

Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa PDP a Sokoto
Ana ta shirin 2023, Masu ruwa da tsakin PDP na Sokoto sun koma APC | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa da Bashar Abubakar, hadimin Sanata Aliyu Wammako ya fitar a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba, wannan ci gaba da suka samu ya faru ne a karamar hukumar Isa ta jihar.

Kara karanta wannan

Ta karewa APC a jihar a wata Arewa, dan takarar sanata da masoyansa sun koma ADC

Daga wasu yankuna suka taso?

Bashar ya kuma bayyana cewa, wadanda suka sauya shekan zuwa APC sun kasance shugabanni kuma masu ruwa da tsaki a yankunan Turba, Bafarawa da Bargaja da dai wasu fitattun yankunan jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, wadanda suka sauyan shekan sun samu tarba daga dan takarar sanatan mazabar, Alhaji Ibrahim Lamido a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar.

Bashar ya naqalto Lamido na ba sabbin mambobin jam'iyyar tabbacin samun wuri a APC, kuma za a dauke su kamar tsoffin mambobinta a ko'ina a kasar nan.

Dan takarar sanatanm wanda Alhaji Kabiru Sarkin-Fulani ya wakilta, shugaban APC na karamar hukumar Goronyo ya marabce su matuka zuwa jam'iyyar.

Ya kuma yaba da irin jajircewar da suka yi na daukar wannan mataki, sannan ya kalubalance su da su kara kokari wajen ciyar da APC da ma jihar baki daga gaba.

Kara karanta wannan

2023: Mambobin APC Sama da 200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Yankin Wani Gwamnan Arewa

Da suke bayyana dalilin barin PDP, wadanda suka sauya shekan sun ce sam sun rasa kwarin gwiwar hango nasara a PDP a zabe mai zuwa.

Dan Takarar Sanatan APC a Kogi, Da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar ADC

A wani labarin, dan takarar sanata a jam'iyyar APC a jihar Kogi, Oni Christopher Tosin da dimbin masoyansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.

Wannan ya faru ne a wani bikin da ya samu halartar jiga-jigai irinsu Leke Abejide, mamban majalisa mai waliltar Yagba a majalisar kasa da aka gudanar a Egbe, karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar ta Kogi.

Leke Abejide ya bayyana jin dadinsa da samun Tosin a matsayin mamban jam'iyya, kuma a cewarsa, jam'iyyar ta yi babban kamu da samunsa, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel