'Na Sadaukar da Rayuwata saboda Shi': Wike Ya Faɗi Taimakon da Ya Yiwa Amaechi

'Na Sadaukar da Rayuwata saboda Shi': Wike Ya Faɗi Taimakon da Ya Yiwa Amaechi

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya sadaukar da rayuwarsa saboda tsohon gwamna, Rotimi Amaechi
  • Wike ya ce ya sa rayuwarsa cikin hadari domin tabbatar da Amaechi ya zama gwamnan Ribas a zaben shekarar 2007
  • Wike ya zargi Amaechi da rashin gaskiya da halaye marasa kyau, yana mai cewa “Amaechi ya boye kadarori a Abuja da Port Harcourt

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan halaccin da ya yi wa Rotimi Amaechi.

Wike ya ce ya sa rayuwarsa cikin hadari kuma ya kashe duk abin da ya mallaka don ganin Amaechi ya zama gwamnan jihar Rivers a 2007.

Wike ya caccaki Rotimi Amaechi kan siyasa
Wike ya fadi taimakon da ya yiwa Amaechi a siyasa. Hoto: Nyesom Wike, Rotimi Amaechi.
Asali: Facebook

Nyesom Wike ya sake tabo Rotimi Amaechi

Yayin wata hira da Channels TV a shirin 'Politics Today' ranar Juma'a da dare, Wike ya zargi Amaechi da yaudara, riya da rashin amana a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ce duk da Rotimi Amaechi yana nuna kamar ba shi da kudi, yana da gidaje a wurare masu tsada a Abuja da Port Harcourt.

A cewarsa:

“Zan gaya muku inda gidansa yake a Guzape, inda nake zaune. Ba za ka mallaki wadannan kadarori ba ka ce talaka ne."

'Yadda Amaechi ya so a kore ni' - Wike

Ya ce halin Amaechi da batun neman shugabancin kasa abin kunya ne, yana tambayar ko hakan ya dace da wanda ke son mulkin Najeriya.

Ya ba da labarin wani lokaci da suka fuskanci cikas lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, inda ya ce Amaechi ya yi yunkurin korarsa daga siyasa.

“Abin takaici ne. Yaya mutum kamar shi zai rika irin wadannan abubuwa? Ko maganar matarsa ma ban so."
“Amaechi ya dauka yana min alheri lokacin da ya kokarin cire ni. Amma da ni ne kawai ya samu nasara. Ni ne DG, ba zan lamunce ba.”

- Cewar Wike

Wike ya gorantawa Amaechi kan taimakonsa da ya yi
Wike ya fadi gagarumin taimako da ya yi wa Amaechi. Hoto: Nyesom Ezonwe Wike.
Asali: Facebook

Wike ya fadi yadda ya taimaki Amaechi

Wike ya ce ya kai har da kwashe iyalansa saboda tsoron abin da zai faru yayin da yake kokarin ceto Amaechi daga matsala ta siyasa.

Ya ce Amaechi ya tarbe shi a filin jirgin Ghana cikin hawaye da hular kwano a kai, yana nuna irin hatsarin da suka shiga.

Wike ya ce ya kashe komai da ya mallaka don taimaka wa Amaechi ya zama gwamna, yana bukatar wasu su tabbatar da gaskiyarsa.

“Mun kwashe Amaechi zuwa Ghana, nan na fara sa ‘baban riga’. Na ce wa matata ta kwashe ‘ya’yana, idan na mutu, haka Allah ya so.
“Ka tambayi Marcus Nneji, Bello Adoke, Magnus Abbey ko Idozu. Duk dukiyata na sadaukar da ita. Amaechi babban makaryaci ne.”

A karshe ya ce bai taba neman iko ko kudi a gwamnatin Amaechi ba, kawai ya bukaci a ba shi matsayin shugaban ma’aikata ne kawai.

Wike ya yi magana kan hadaka

Kun ji cewa Nyesom Wike ya ce kawancen ADC ba shi da ƙarfi ko daidaito don fuskantar Bola Tinubu a 2027, inda ya fadi jam'iyyar za ta iya karawa da APC.

Tsohon gwamnan Rivers ya zargi David Mark da yunkurin karɓar shugabancin PDP kafin ya koma shugaban rikon ƙwarya na ADC.

Wike ya soki Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai, ya ce suna yawan sauya jam’iyya don biyan buƙatar kansu kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.