Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Rufa-rufa Wajen Bayar Da Kwangilar Titin Legas-Kalabar

Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Rufa-rufa Wajen Bayar Da Kwangilar Titin Legas-Kalabar

  • Tsohon Matiamakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da rufa-rufa wajen bayar da kwangilar babban titin Legas-Kalaba
  • Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar titin mai tsawon kilomita 700 ga kamfanin Hitech, kuma titin zai ratsa ta cikin jihohi tara
  • Atiku Abubakar ya ga baiken gwamnatin na kin bawa wasu kamfanonin damar nuna sha'awar gudanar da aikin titin, da kuma kin bayyana ainihin kudin kwangilar

Abuja, Najeriya- Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ƙalubalanci hanyar da gwamnatin tarayya ta bi wajen bayar da kwangilar babban titin Lagos-Calabar ga kamfanin Hitech Construction Company Limited kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Atiku ya yi zargin akwai ƙumbiya-ƙumbiya a hanyar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya bi wajen bayar da kwangilar titin mai tsawon kilomita 700.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da rufa-rufa wajen bayar da kwangilar babban titin Legas-Kalaba
Atiku Abubakar ya soki Tinubu kan aikin titin Legas-Kalaba Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya fitar ta shafin facebook, ya sanyawa hannu, ya ce:

"Gwamnatin Tinubu ta kuma bayyana halinta na rufa-rufa wajen gudanar da ayyuka, kamar yadda ta bayar da kwangilar titin Lagos-Calabar mai tsawon kilomita 700."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, an bayar da kwangilar ba tare da bawa wasu kamfanonin damar neman kwangilar aikin ba kamar yadda doka ta sahale.

Haka kuma Shugaba Tinubu bai nemi amincewar majalisar zartarwa ta tarayya ba.

Daga zarge-zargen da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP ya yi, Atiku ya zargi Ministan ayyuka, Dave Umahi da ƙin bayyana aihinin kuɗin kwangilar hanyar ba.

A kalamansa:

" A watan Satumbar 2023, makonni kaɗan bayan naɗinsa a matsayin Ministan ayyuka, Injiniya Dave Umahi ya sanar da bayar da kwangilar ga Gilbert Chagoury Hitech Construction Company Limited (Hitech) ba tare da shaidar bawa wasu kamfanonin damar nuna sha'awar yin aikin ba, ko sahalewar majalisar zartarwa ba."

Kara karanta wannan

Ba a haka: Atiku ya taimakawa Tinubu da shawarwari kan karin kudin wutar lantarki

Atiku Abubakar ya kuma ga rashin dacewar yadda ministan ya ƙi bayyana batutuwa masu muhimmanci kan kwangilar.

Umahi, a wancan lokaci ya bayyana cewa ana gudanar da aikin ne haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƴan kasuwa.

Yadda aikin zai gudana a tsarin PPP

A wannan tsarin na haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƴan kasuwa , Kamfanin Hitech zai gudanar da aikin titin, amma zai ci gaba da gudanar da shi har sai ya mayar da kuɗin da ya kashe da kuma riba.

A cewar Ministan ayyuka Umahi:

"Kamfanin Hitech ya samo hanyar samun kuɗi. Sun riga sun samu kuɗi, kuma wannan labari ne mai kyau domin ba za mu ɓata lokaci wajen magana, da gudanar da tarurruka ba."

Amma Atiku Abubakar ya ce yadda Dave Umahi a watan Maris ɗin 2024 ya nemi majalisar zartarwa ta amince da fitar da Naira tiriliyan 1 da biliyan 6 domin biyan kamfanin Chagoury a matsayin kuɗin fara aikin da zai gudana a ajihar Legas ya bawa ƴan Najeriya mamaki matuƙa.

Kara karanta wannan

Bayan gama bincike, tsohon gwamnan CBN ya gamu da sabuwar matsala babba a mulkin Tinubu

Atiku ya ce:

" Wannan aikin karo na farko zai faro daga Eko Atlantic City dake Ahmadu Bello Way, Victoria Island zai ƙare ne a Lekki Deep Sea Port, Ibeju-Lekki, tsawon kilomita 47.47. Har yanzu gwamnatin Tinubu ta ƙi bayyana kuɗin aikin baki ɗayan sa."

Atiku ya na ganin idan za a biya Naira tiriliyan 1 da biliyan 6 a aikin kilomita 47.47, hakan na nufin za a gina kowane kilomita akan Naira biliyan 22 da miliyan biyar.

Ya ce hakan na nufin:

"Titin mai tsawon kilomita 700 zai kama akan Naira tiriliyan 15 da biliyan 7 ko kuma Dala biliyan 12 da mikiyan 56."

An bada kwangilar titi kan maƙudan kuɗi

A watan Maris ne gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar babban titi wanda zai taso da Lagos, ya kuma ratsa ta cikin jihohi tara.

Duk da gwamnatin ba ta bayyana adadin kuɗin aikin ba, Ministan ayyuka Dave Umahi ya ce ba za mu lamunci wasa da aikin titin ba idan an fara shi.

An dai bawa kamfanin Hitech kwangilar gudanar da aikin titin mai tsawon kilomita 700.

Asali: Legit.ng

Online view pixel