Rigima Ta Ɓarke a APC bayan Murabus ɗin Ganduje, An Dakatar da Shugaban Jam'iyya a Nasarawa
- Ƙasa da mako guda bayan Abdullahi Ganduje ya yi murabus, sabon rikici ya ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Nasarawa
- Shugabannin APC na gundumar Gayam sun sanar da dakatar da shugaban jam'iyya na jiha, Hon. Aliyu Bello bisa zarginsa da cin amana
- Mai magana da yawun APC a Nasarawa ya yi ikirarin cewa wannan makircin wani ɗan takara ne da ke son kawar da shugabancin Aliyu Bello
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Rahotanni sun nuna cewa shugabannin APC a gundumar Gayam sun dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Nasarawa, Aliyu Bello nan take.
Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan jagororin APC a matakin jihar Nasarawa sun mara masa baya ta hanyar kaɗa kuri'ar amincewa da jagorancinsa.

Asali: Facebook
Channels tv ta tattaro cewa an dakatar da shugaban APC na Nasarawa ne bisa zargin cin amana da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta dakatar da shugabanta na Nasarawa
Shugaban APC na gundumar Gayam, Ibrahim Ilyasu, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ranar Talata a Lafia, babban birnin Nasarawa.
A cewarsa, sun dakatar da Aliyu Bello ne bayan amincewar duka shugabannin APC na gundumar Gayam saboda zargin da ake masa na karya dokokin jam'iyya.
Ibrahim Iliyasu ya ce ana zargin shugaban APC na jihar Nasarawa da karya Sashe na 21 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, cewar rahoton Daily Trust.
Ya ce:
"Dogaro da ƙarfin ikon da doka ta ba shugabannin gunduma bisa tanadin sashe na 21 (D) (i)-(iii) na kundin tsarin mulkin APC, mun yanke shawarar dakatar da Hon. Aliyu Bello nan take.
Meyasa aka dakatar da shugaban APC?
Ibrahim ya ce Aliyu Bello ya aikata ayyukan cin amanar jam’iyya, da ya haɗa da kamfe da goyon baya ga wani ɗan takarar wata jam’iyya, wanda hakan ya zubar da kimar APC.
"Muna da hujjoji masu ƙarfi da rahotanni da ke nuna cewa ka yi kamfe tare da goyon bayan ɗan wata jam’iyya ta daban.
"Wannan ya saɓa Sashe na 21 (0), (ii), da (vii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya haramta duk wani abu da zai janyo wa jam’iyya ƙiyayya, raini, ko zubar da mutunci.”
“Abin da ka aikata ya jawo wa jam’iyya abin kunya, ya ci mutuncin ƙoƙarin da muke yi a tare, kuma ya karya ƙa’idar biyayya da ladabi na jam’iyya.”
- Inji Ibrahim Iliyasu.

Asali: Twitter
Ibrahim ya ƙara da cewa dakatarwar ta fara aiki nan take, tare da kira ga Aliyu Bello ya daina bayyana kansa a matsayin ɗan APC a gundumar Gayam.
Kakakin APC a Jihar Nasarawa, Otaru Douglas, ya zargi wani ɗan takarar gwamna da ɗaukar nauyin wannan dakatarwar a matsayin wani yunkuri na kawar da shugaban jam’iyyar daga muƙaminsa.
APC ta sha alwashin kai Tinubu ga nasara a 2027
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi tazarce zuwa zango na biyu a zaɓen 2027 duk da shirin ƴan adawa.
Wannan martani na APC na zuwa ne bayan haɗakar ƴan adawa ta zaɓi jam'iyyar ADC a matsayin wacce za ta tunkari zaɓen 2027.
Duk da sukar da jam’iyyar ke fuskanta a fannoni daban-daban, APC na ganin cewa za ta sake samun nasara a zaɓe na gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng