Shugaba Tinubu Ya Jagoranci Bill Gates da Otedola zuwa Matatar Dangote
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu da Bill Gates sun ziyarci matatar mai ta Dangote da ke Lekki, wacce darajarta ta kai Dala biliyan 20
- Fitaccen attajirin Najeriya, Femi Otedola ya bayyana cewa matatar ita ce babban abin mamaki da aka samar a wannan zamani
- Haka kuma shugaban ya kaddamar da wasu ayyuka a bakin teku, wanda ya fara daga tashar ruwa ta teku zuwa Epe da Ijebu-Ode
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Shugaban ƙasa, Bola Tinubu tare da fitaccen attajirin Amurka kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates, sun ziyarci matatar Dangote a Legas.
Wannan matatar, wacce darajarta ta kai Dala biliyan 20, ita ce mafi girma a duniya da ke aiki da tsari guda ba a rarrabe kamar wasu manyan matatu ba.

Asali: Twitter
A cikin saƙon da fitaccen attajirin Najeriya, Femi Otedola ya wallafa a shafinsa na X, ya ce har da shi da kuma Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA Group a tawagar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar Bola Tinubu ta jinjinawa matatar Dangote
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Mista Femi Otedola ya bayyana matatar Dangote a matsayin abin mamaki mafi girma a zamanin nan.
Ya kuma bayyana ziyarar da suka kai mashahurin kamfanin Dangote da cewa abin tarihi me mai cike da darussa.
Mista Otedola ya ce:
“A yau, na kasance cikin wani babban taro na tarihi. Shugaban ƙasarmu mai hangen nesa, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara zuwa matatar mai da sinadarai ta Dangote mai darajar Dala biliyan 20 — mafi girma a duniya cikin nau’inta — wanda ɗan’uwana kuma abokina, Aliko Dangote, ya gina."
Tinubu ya kaddamar da sababbin ayyuka
A ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya kaddamar da aikin gyaran hanyar da ke haɗa tashar ruwa ta teku mai zurfi ta Lekki da Epe zuwa Ijebu-Ode.
Otedola ya ce tun shekaru fiye da 20 da suka wuce, lokacin da Tinubu ke matsayin gwamnan Legas, ya hango kafa cibiyar kasuwanci mai faɗi a bakin teku.

Asali: Twitter
Ya ce:
“A yau, wannan hangen nesa ya tabbata. “Shugaba nagari yana jagorantar jama’a zuwa inda dole su je, koda kuwa ba su so. Wannan shi ne shugaban ƙasa Tinubu.”
Femi Otedola ya ƙara da cewa:
“Shugaban ƙasa ya kuma kaddamar da jerin sababbin ayyukan hanyoyi da aka kammala.”
An kira Dangote 'shugaba' a gaban Tinubu
A baya, mun ruwaito cewa yayin wani taro da aka gudanar a jihar Legas, fitaccen ɗan kasuwa Aliko Dangote ya ja hankalin mai gabatar da taro bisa kuskuren kiransa da “shugaba”.
Dangote ya gyara kuskuren cikin dariya da barkwanci, yana mai cewa bai kamata a kirashi da shugaba a gaban Shugaban kasa Bola Tinubu ba, sai dai jagoran kamfani.
A yayin taron, Dangote ya sanar da cewa an saka wa titin da ke kaiwa zuwa Matatar Dangote suna hanyar Bola Ahmed Tinubu domin girmama shugaban ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng