Rigima Ta Ɓalle a APC kan Alaƙar Tinubu da Gwamnonin Adawa Ana Shirin Zaɓe

Rigima Ta Ɓalle a APC kan Alaƙar Tinubu da Gwamnonin Adawa Ana Shirin Zaɓe

  • 'Yan APC a Osun da Anambra na nuna damuwa da ganawar Gwamna Ademola Adeleke da Charles Soludo da Bola Tinubu
  • Wasu jiga-jigan APC na Osun sun fadi cewa Adeleke na neman shiga jam'iyyar saboda tsoron faduwa, amma suka ce ba za su yarda ba
  • A Anambra, APC ta musanta cewa Tinubu ya amince da Soludo, tana cewa Shugaban ya bukaci su karbe jihar a zaben 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mambobin jam’iyyar APC a jihohin Osun da Anambra sun nuna rashin jin daɗinsu kan alaƙar Shugaba Bola Tinubu da gwamnoninsu.

Wasu mambobin jam’iyyar sun ce goyon bayan Tinubu ga Gwamnoni Ademola Adeleke (Osun) da Chukwuma Soludo (Anambra) na iya cutar da ‘yan takarar APC a gaba.

APC ta koka kan alaƙar Tinubu da wasu gwamnoni
An fara samun matsala kan alaƙar Tinubu da gwamnonin adawa. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Yan APC sun koka kan alaƙar Tinubu, gwamnoni

A jihar Osun, wasu shugabannin APC da ke biyayya ga Ministan Harkokin Ruwa, Gboyega Oyetola, sun nuna rashin jin daɗi kan ziyarar Adeleke zuwa gidan Tinubu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ranar 3 ga Yuni, Adeleke tare da dan uwansa, Dr Deji Adeleke, da ɗan uwansu mawaki Davido sun gana da Tinubu a Lagos.

Ziyarar Adeleke ta ƙara janyo rade-radin cewa yana shirin komawa APC, musamman bayan da wasu gwamnonin PDP suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

A wani taron manema labarai da tsohon Kakakin Majalisa, Timothy Owoeye ya jagoranta, shugabannin APC sun ce ba su maraba da Ademola Adeleke cikin jam’iyyar.

Sun ce Adeleke yana cikin firgici da fargaba ne, shi ya sa yake neman komawa APC domin gudun faduwa a zabe mai zuwa.

APC a Osun ta caccaki Gwamna Adeleke

Kakakin APC na Osun, Kola Olabisi, ya ce Adeleke ba shi da tabbacin nasara idan ya tsaya takara a PDP, shi ya sa yake neman mafita.

Olabisi ya kara da cewa abubuwan da suka ba Adeleke nasara a zaben 2022 yanzu sun gushe, kuma yana neman shiga APC ne domin cutar da jam’iyyar.

Sai dai kakakin PDP na Osun, Oladele Bamiji, ya ce ‘yan APC na nuna jahilci da girman kai da zargin su kadai ke da Shugaba Tinubu, TheCable ta ruwaito.

Bamiji ya ce ‘yan APC sun manta cewa Tinubu shugaban ƙasa ne, kuma dole ne ya riƙa ganawa da dukkan gwamnonin jihohi ba tare da wariya ba.

Ya ce APC ta Osun ba ta son aiki da kansu, sai dai su nemi Shugaban ƙasa ya taimaka musu wajen kwace mulki da karfin iko.

An soki Tinubu kan alaƙa da gwamnonin adawa
Yan APC sun koka da alaƙar Tinubu da wasu gwamnoni. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Jigon APC ya soki tsarin da ake bi

Wani jigo a APC wanda ya buƙaci a sakaye sunansa ya ce ba daidai ba ne a karɓi Adeleke tare da wulakanta mambobin jam’iyyar na gaskiya.

Ya ce shugabannin jam’iyyar APC a Osun sun damu matuƙa da alaƙar Tinubu da Adeleke, kuma ba su san matsayinsa a zaben 2026 ba.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu mutum ne da ya kamata ka riƙa lura da shi sosai. Ba za ka iya hango matsayinsa a siyasa ba.”
“Ba ma so Adeleke ya shiga APC. Yana son cin gajiyar aikin da muka yi. Mun jima muna jan ragamar siyasa a jihar nan.”

Hukumar zaɓe ta kasa INEC ta bayyana cewa zaben gwamna na Osun zai gudana ranar 6 ga watan Agusta, 2026.

Gwamna ya musanta ziyartar boka kan tazarce

Kun ji cewa Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra ya musanta zargin cewa ya tuntuɓi boka don neman nasarar zaɓe na ranar 8 ga Nuwamba.

Mai magana da yawun gwamnan, Christian Aburime, ya ce bidiyon da ke yawo na barkwanci ne da wani ɗan kwaikwayo ya yi a taro.

Ya ƙara da cewa Soludo na kokarin bunkasa tattalin arzikin jihar, kuma jama’a su ƙaurace wa yaɗa labaran ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.