'Hanya 1 da 'Yan Adawa Za Su Kwace Mulki daga Tinubu,' An ba Su Atiku Shawara

'Hanya 1 da 'Yan Adawa Za Su Kwace Mulki daga Tinubu,' An ba Su Atiku Shawara

  • Kenneth Okonkwo, tsohon kakakin Peter Obi, ya ce dole jam’iyyun adawa su kafa kawance domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Okonkwo ya ce ba zai iya tabbatar da kawance tsakanin Obi da Atiku Abubakar ba, amma za a samu kawance kafin zaben 2027
  • Ya ƙara da cewa babu wani dan siyasa daya tilo da zai iya kayar da Tinubu, don haka ne ya zama wajibi 'yan adawa su kulla kawance

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kenneth Okonkwo, tsohon mai magana da yawun Peter Obi na LP a zaben 2023, ya ce dole ne jam’iyyun adawa su kula kawance domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Fitaccen jarumin da ya koma siyasa ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin.

Kenneth Okonko ya ba su Atiku shawara kan yadda za su iya kwace mulki daga Tinubu a 2027
Kenneth Okonkwo tare da Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya. Hoto: Kenneth Okonkwo
Asali: Facebook

"Dole a samu kawance kafin 2027" - Okonkwo

A tattaunawarsa da Channels TV, Kenneth Okonkwo ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba zan iya tabbatar da kawance tsakanin Peter Obi da Atiku ba, amma yayin da muke tunkarar 2027, na san za a samu kawancen 'yan adawa. Ko tsakanin Obi da Atiku ne, ban sani ba.”

Okonkwo ya ƙara da cewa:

"Dole ne a samu kawance kafin zaben 2027, domin wannan ne kawai zaɓin da 'yan adawa ke da shi idan suna son su karbi mulki."
Da aka tambaye shi ko za a iya kayar da Tinubu ba tare da kawance ba, Okonkwo ya amsa da cewa “a bayyane yake, Tinubu zai lashe zaben cikin sauƙi, ma damar ba kawance."

Yadda 'yan adawa za su kayar da Tinubu

Ya bayyana cewa:

“Ba wani ɗan takara guda ɗaya da zai iya kayar da Tinubu. Dalilin kuwa shi ne, a Najeriya yanzu ba cin zaben ba ne kawai, dole ne ka kare nasararka."

Kenneth Okonkwo ya jaddada cewa dole mutum yana buƙatar manyan mutane (kusoshin kasar) "domin kare nasararka ko da mutane sun zaɓe ka."

Ya ci gaba da cewa:

“Idan jiga-jigan kasar suka haɗu kamar yadda suka yi a zaben 2014 suka kayar da Goodluck Jonathan a 2015, to za su iya karbar mulki daga Tinubu a 2027."
Kenneth Okonkwo ya ce masu sauya sheka zuwa APC na shiga gidan da ke shirin nutsewa kasa
Kenneth Okonkwo tare da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Kenneth Okonkwo
Asali: Facebook

Okonkwo ya ce APC za ta ruguje kafin 2027

Yayin da yake magana kan yawaitar sauya sheƙar 'yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa APC, Okonkwo ya ce masu sauya sheƙar na tunanin za a yi murdiyar zaɓe ne a 2027.

Sai dai ya bayyana cewa APC za ta fuskanci kalubalen da zai iya sanya wa ta ruguje nan ba da jimawa ba, inda ya ce jam’iyyar "ta dauki hanyar nutsewa."

“Dalilin su na shiga wata jam’iyya, musamman jam’iyya mai mulki, shi ne kawai saboda tunanin cewa za a rubuta sakamakon zaɓe a 2027, ba wani abu ba.

"Abin mamaki ne mutane su ga gida yana nustewa kuma gudu su nemi mafaka a cikinsa, saboda APC gida ne da ke kan nutsewa kasa."

- Kenneth Okonkwo.

Kalli bidiyon a kasa:

An nemi Jonathan ya fito takara a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Kungiyar NRMO ta yi kira ga Goodluck Jonathan da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 domin hada kan Najeriya.

Shugaban NRMO, Dr. Jibril Mustapha, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaba wanda zai magance matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro, rashin aikin yi da ta’addanci.

A cikin hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Bayelsa ta yanke a 2022, an tabbatar da cewa Jonathan na iya sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.