An Shiga Tashin Hankali, Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Sume ana tsaka da Taron APC
- Magoya bayan APC sun shiga firgici da tashin hankali da shugaban karamar hukumar Bariga ta jihar Legas, Kolade Alabi ya sume a wurin taron
- Kolade, wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON) ya yanke jiki ya faɗi a taron masu ruwa da tsakin APC a Legas
- An ruwaito cewa likitoci da hadimansa sun yi ƙoƙarin dawo da shi hayyacinsa kafin daga bisani aka garzaya da shi asibiti mafi kusa da sakatariyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Legas - An shiga wani hali na firgici da rudani a ranar Laraba da rana, yayin wani taron masu ruwa da tsakin APC da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke titin Acme, jihar Legas.
Mahalarta taron sun shiga yanayin tashin hankali lokacin da shugaban ƙaramar hukumar Bariga, Alhaji Kolade David Alabi ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taron.

Asali: Twitter
Vanguard ta tattaro cewa Alabi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Legas ya ya suma a wurin taron lokacin da yake jawabi ga magoya bayan APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban karamar hukuma ya suma a Legas
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:10 na rana, yayin da Hon. Kolade Alabi ke tsaka da gabatar da jawabi ga mahalarta taron, inda nan take ya zube ƙasa a sume.
Taron dai ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da shugabannin jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na jihar Legas da ma kasa baki ɗaya.
Sai dai faɗuwar shugaban ƙaramar hukumar ta dakatar da taron na ɗan lokaci, yayin da jami’an lafiya da masu tsaron lafiyar Kolade suka yi saurin zuwa wurin don ba shi agajin gaggawa.
Wane hali shugaban ALGON ke ciki?
Shaidun gani da ido sun ce an shafe kimanin mintuna kafin a samu nasarar farfado da shi, inda daga bisani aka garzaya da shi zuwa wani asibiti mafi kusa.
Duk da cewa ba a fitar da cikakken bayani game da halin da yake ciki ba a hukumance, majiyoyi sun bayyana cewa yana ƙarƙashin kulawar likitoci kuma alamu na nuna yana samun sauki.

Asali: Twitter
‘Yan jam’iyyar APC da suka halarci taron sun nuna damuwarsu, tare da addu’a da fatan Allah ya ba shi lafiya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wani jigo a jam’iyyar ya ce, "Kolade mutum ne mai himma da kishin ci gaban ƙasa. Wannan lamari abin firgitarwa ne, amma muna godiya ga Allah da ba a rasa rai ba."
APC ta cire sunan ɗan takara a Legas
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta cire sunan ɗan takarar kujerar shugaban ƙaramar hukuma a jihar Legas saboda zargin aikata rashin gaskiya.
APC ta zare sunan ɗan takararta na karamar hukumar Eti-Osa ta Gabas, Samad Ogunbo ne saboda ta gano yana karɓar albashi biyu daga gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa an samu Ogunbo yana aiki a hukumar SUBEB, sannan kuma ya na riƙe da matsayin mai sanya ido a wata karamar hukuma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng