'Ka Yi Kadan': Sule Lamido Ya Mayar da Martani ga El-Rufai game da Kalamansa
- Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Nasir El-Rufai ba ya da darajar shugabanci, ba zai iya janyo ‘yan PDP su bi shi SDP ba
- Lamido ya ce El-Rufai bai cancanci gayyatar manyan ‘yan adawa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba domin ba shi da kishin kasa
- Ya kara da cewa PDP ce ta haifi El-Rufai, bai kamata ya koma baya ya soke jam’iyyar da ta dauke shi ba
- Sule Lamido ya jaddada cewa shugabanci na gaskiya yana buƙatar natsuwa da hangen nesa, ba fushi da son zuciya ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya mayar da martani ga Nasir El-Rufai kan kiran da ya yi wa ‘yan siyasa su biyo shi SDP.
Lamido ya ce kwata-kwata El-Rufai ba shi da daraja kuma bai cancanci kiransu zuwa jam'iyyarsa ta SDP a halin yanzu.

Asali: Facebook
Yadda El-Rufai ya kira jiga-jigan Najeriya zuwa SDP
A wata hira da BBC Hausa, Lamido ya soki wannan kira, yana cewa El-Rufai ba ya da kishin al’umma, balle ya gayyaci ‘yan PDP su bi shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta ruwaito El-Rufai na neman Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola su bar jam’iyyunsu su koma SDP.
Lamido ya ce:
"Wannan raini ne, don boda Allah, ta yaya El-Rufai kalle mu a PDP ya ce zai kira mu wata jam'iyya.
"Ya ce ya fadawa Buhari, ta yaya za ka kalle ni ka ce na bi umarnin Buhari ba, idan dai har haka ne me yasa ya je wurin Buhari tun da ya ce su ne manya."

Asali: Facebook
Sule Lamido ya yi wa El-Rufai martani mai zafi
Lamido ya ce hakan kamar jika ne yana cewa kakansa bai san komai ba, duk da cewa PDP ce tushen El-Rufai.

Kara karanta wannan
Matsalar Obasanjo da Atiku: Kalaman El-Rufai sun ba da mamaki kan rigimarsu a baya
Ya kara da cewa El-Rufai ya taba cewa babu manya a Najeriya, amma yanzu yana kokarin neman goyon bayan su.
Lamido ya bayyana cewa ya taba zama sakataren SDP, amma bai ga wani laifi da PDP ke da shi yanzu ba.
Ya ce:
"Duk rikicin da PDP take ciki, a nan aka haife shi. Idan ya ce PDP ta mutu to a nan ne asalinsa, nan ne aka haife shi, za a ce El-Rufai ministan PDP ne, duk bin da ka mallaka duniya PDP ce."
Lamido ya ce da yana son barin PDP, da tuni ya bar ta tun lokacin da aka kafa APC, amma ya nace ya zauna.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tun farko ya san APC ba za ta yi nasara ba, kuma hakan ya tabbatar da hasashensa.
Ya ce shugabanci ba a yin sa da fushi ko son zuciya, dole a kasance da hangen nesa da natsuwa.
Sule Lamido ya caccaki salon mulkin Tinubu
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce mulkin APC ya yi kamanceceniya da na Fir’auna da aka yi a tarihi.
Sule Lamido ya ce talauci ya zama makami, yunwa kuma tana yawo a titunan kasar wanda ke illa ga al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng