Abin da APC Ta ce bayan Ganawar Atiku, Obasanjo da Ake Zargin Shirin Kada Tinubu ne

Abin da APC Ta ce bayan Ganawar Atiku, Obasanjo da Ake Zargin Shirin Kada Tinubu ne

  • Jam’iyyar APC ta yi martani kan haduwar Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a ranar Litinin dinnan
  • Jam'iyyar ta ce hadakar Obasanjo da Atiku ba barazana ba ce ga tazarcen Bola Tinubu a 2027, yayin da suka ci gaba da shirye-shiryensu na siyasa
  • Atiku da wasu manyan ‘yan siyasa sun gana da Obasanjo a Abeokuta, amma APC ta bayyana su a matsayin “marasa aikin yi” marasa tasiri
  • Obasanjo da Atiku sun yi irin wannan kokari a baya, amma APC ta ce jam’iyyarta ba ta cikin rikici, kuma tana mayar da hankali kan nasararta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana matsayarta kan haduwar Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo sa wasu manyan yan siyasa.

APC ta ce hadakar Olusegun Obasanjo da dan takarar PDP na 2023, Atiku Abubakar, ba barazana ba ce ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

NNPP: "Har yanzu Kwankwaso, Abba halastattun 'yan jam'iyya ne"

APC ta mayar da martani game da haduwar Atiku da Obasanjo
Jam'iyyar APC ta ce rashin aikin yi ke damun Atiku da sauran masu haɗaka kan zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

An yi hasashen dalilin ganawar Atiku, Obasanjo

Sakataren jam'iyar APC ta kasa, Sanata Ajibola Basiru shi ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa bayan Atiku ya jagoranci wata tawaga mai karfi, ciki har da Aminu Tambuwal, da tsohon gwamnan Cross River, Sanata Liyel Imoke, zuwa ganawar.

Tawagar ta isa gidan Obasanjo da ke cikin dakin karatu na Olusegun Obasanjo da misalin karfe 12:37 na rana, inda dattijo Otunba Oyewole Fasawe ya tarbe su.

Duk da cewa cikakkun bayanan ganawar ba a bayyana ba, ana hasashen cewa ba za ta rasa nasaba da burin Atiku na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko ganawar tana da nasaba da burinsa na 2027, Atiku ya ce:

“Ziyarar girmamawa ce kawai, ba batun siyasa ba.”

Sai dai ganawar ta janyo rade-radin yiwuwar wata hadaka, inda wasu ke ganin Obasanjo na iya jagorantar sabuwar kungiya ta siyasa.

Kara karanta wannan

'Me suke kullawa?': Atiku ya ja zugar manyan 'yan siyasa, sun gana da Obasanjo

Martanin APC game da ganawar Atiku, Obasanjo

Basiru ya fadi haka yayin da yake tsokaci kan ganawar da aka yi tsakanin Obasanjo da tsohon mataimakinsa, Atiku, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Sai dai Basiru ya yi watsi da ganawar, yana cewa:

“Marasa aikin yi ne kawai suke yin irin wadannan taruka, mu a APC muna mayar da hankali kan nasarar zaben gwamna a Anambra.”
“Jam’iyyar APC ba ta cikin wata matsala, kuma muna da manyan mutane da za su iya cin zabe ba tare da wata barazana ba.”

Atiku ya taba kokarin hada kan jam’iyyun adawa a baya, musamman a 2024, amma bai cimma nasara ba yayin da APC ke ci gaba da karfafa mulkinta.

A gefe guda, Obasanjo ya taba marawa Atiku baya a zaben 2019, yana mai cewa yana da kwarin gwiwa cewa zai fi Muhammadu Buhari kokari.

2027: Kwankwaso ya yi wata ganawa da Aregbesola

Kara karanta wannan

Matakin da APC ta dauka kan 'ya'yanta da suka bauɗe, suke cin mutuncin Tinubu, Ganduje

Kun ji cewa rahotanni sun nuna Rabiu Kwankwaso yana kokarin jawo tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, domin samun goyon baya a Kudu.

A karshen mako da ya wuce, Sanata Kwankwaso ya gana da Aregbesola a gidansa da ke Legas a wani zama da suka yi da ya ja hankalin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.