Bayan Kwashe Dogon Lokaci Suna Tattaunawa, Atiku Ya Fadi Dalilin Ziyartar Obasanjo

Bayan Kwashe Dogon Lokaci Suna Tattaunawa, Atiku Ya Fadi Dalilin Ziyartar Obasanjo

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun
  • Atiku Abubakar da tsohon shugaban ƙasan sun ɗauki dogon lokaci suna tattaunawa a kan batutuwan da su kaɗai kawai suka sani
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ƙi yin magana kan batun siyasa bayan sun kammala taro da Obasanjo tare da wasu manyan PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP ya ziyarci Olusegun Obasanjo ne a ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairun 2023, a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Atiku ya ziyarci Obasanjo
Atiku ya sanya labule da Obasanjo Hoto: @Rasheethe
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya yi magana da manema labarai bayan sun kammala tattaunawa da tsohon shugaban ƙasan.

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya ziyarci Obasanjo

Atiku Abubakar dai ya isa ɗakin karatu na shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (OOPL) da ke birnin Abeokuta da misalin ƙarfe 12:36 na rana, tare da wasu jiga-jigan ƴan siyasa.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP ya samu tarba daga wajen na hannun daman Obasanjo, Otunba Oyewole Fasawe.

A cikin tawagar Atiku, akwai tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke, tsohon gwamnan jihar Sokoto.

An kuma ga Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi.

Bayan isowarsa, Atiku kai tsaye ya shiga taron sirri da tsohon ubangidansa, wanda ya ɗauki kusan awa ɗaya da rabi.

Meyasa Atiku ya ziyarci Obasanjo?

Bayan kammala taron, wanda aka gama da misalin ƙarfe 2:11 na rana, Atiku ya fito inda ya yi wa manema labarai bayanin cewa ziyarar tasa ta ban girma ce kawai, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Me suke kullawa?': Atiku ya ja zugar manyan 'yan siyasa, sun gana da Obasanjo

Sai dai, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa ba zai yi magana kan siyasa ba, duk kuwa da irin tambayoyin da manema labarai suka yi masa.

"Ziyara ce kawai ta ban girma, ba zan yi magana a kan siyasa ba."

- Atiku Abubakar

A cikin ƴan kwanakin nan dai, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan da wasu manyan shugabannin jam’iyyun adawa sun riƙa gudanar da tarurruka kan yiwuwar kafa ƙawance gabanin zaɓen 2027.

Atiku ya yi wa gwamnatin Tinubu shaguɓe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi wa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu, shaguɓe.

Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatin tarayya da ka da ta bari kuɗaɗen da aka ware domin harkokin kiwon lafiya a kasafin kuɗi su tafi a banza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng