Tuna Baya: Yadda Naja'atu Ta Yi Wa Nuhu Ribadu Kamfe a 2011, Ta Yabawa Kwarewarsa

Tuna Baya: Yadda Naja'atu Ta Yi Wa Nuhu Ribadu Kamfe a 2011, Ta Yabawa Kwarewarsa

  • An tono yadda Naja’atu Muhammad ta goyi bayan Nuhu Ribadu a takararsa ta shugaban kasa a shekarar 2011
  • An gano Hajiya Naja'atu tana yabon kwarewarsa da mutuncinsa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba
  • A lokacin, ta soki jam’iyyar PDP kan gazawarta wajen shawo kan matsalolin ƙasa, tana kira ga matasa su tashi tsaye
  • Wannan na zuwa ne yayin da a yanzu suka babe har Naja'atu ke sukar Ribadu saboda goyon bayan Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yar gwagwarmaya, Naja'atu Muhammad tana daga cikin wadanda suka goyi bayan takarar Nuhu Ribadu a 2011.

An gano Naja'atu a wancan lokaci tana yaba kwarewarsa a takarar shugaban kasa ba tare da bambancin addini ko kabila ba.

Kara karanta wannan

'Yar hassada ce': Musa Kwankwaso ya soki Naja'atu, ya jero manyan da ta zaga

An tono yadda Naja'atu ke yabawa Ribadu kan kwarewarsa
Naja'atu Muhammad ta yi wa Nuhu Ribadu kamfe a 2011 kafin fara takun-saka da shi a yanzu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

2011: Naja'atu ta yi wa Nuhu Ribadu kamfe

Daily Trust ta ce Naja'atu ta yaba wa Ribadu inda ta ce Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so, ya ba Ribadu shugabancin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribadu da ke zaune a gefenta ya yi murmushi tare da jin dadi kan goyon bayanta a takararsa karkashin jam'iyyar AC.

“Allah, mai ba da mulki ga wanda ya so, ya ba Ribadu shugabancin Najeriya.
“Muna zaɓen Ribadu ba don yana Bahaushe ko Fulani ba, ba don yana Musulmi ba, sai don shi mutumin kirki ne."

- Naja'atu Muhammad

A wancan lokaci, Muhammad ta soki jam’iyyar PDP kan gazawarta wajen shawo kan manyan matsalolin ƙasa, tana cewa lokaci ya yi da za a daina gunaguni, a dauki mataki.

“Tun daga 1999, fiye da mutanen da suka mutu a yakin basasa sun mutu a ƙarƙashin PDP, an kashe su a tarzomar addini, a haɗurran hanya, a cututtukan da za a iya magancewa.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

“Matasan ƙasa, ku ne kashi 80% na yawan jama’a, amma kuna zama shiru kuna guna-guni, idan kuna guna-guni, to kun zama wawaye ko munafuki, Ku fito, ku faɗi gaskiya wannan lokaci namu ne.”
“Suna cewa Jonathan yana da ‘Goodluck.’ Me ya yi? Me ya yi har ya zama mataimakin shugaban ƙasa? Babu komai! Sai dama, me ya yi don ya zama mataimakin gwamna? Babu komai! Gwamnansa ne aka tsige. ‘Goodluck’ gare shi, ‘Bad luck’ ga Najeriya.”

- Naja'atu Muhammad

Haka Naja’atu Muhammad ta yi wa Nuhu Ribadu kamfen a 2011 lokacin da ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin AC.

Naja'atu Muhammad ta yi wa Ribadu martani

A wani labarin, Hajiya Naja’atu Muhammad ta jaddada cewa ba ta yi karya ba, kuma babu abin da zai sa ta janye kalamanta a kan Nuhu Ribadu.

Ta bayyana cewa kalaman da ta jingina wa Malam Nuhu Ribadu sun tabbata, domin har yanzu suna nan a shafukan yanar gizo.

Kara karanta wannan

'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar

Hakan ya biyo bayan barazanar da Ribadu ya yi mata da kuma neman ta janye kalamanta kan abin da ta fada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.