Ondo: Rigima Ta Barke Yayin Zaben Fidda Gwanin Jami'yyar APC, an Lalata Komai

Ondo: Rigima Ta Barke Yayin Zaben Fidda Gwanin Jami'yyar APC, an Lalata Komai

  • Yayin da ake gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar Ondo, rigima ta barke inda wasu suka tarwatsa zaben da ake gudanarwar
  • Wasu magiya bayan dan takarar gwamna a zaben sun tarwatsa masu zabe tare da lalata komai da aka shirya a wurin gudanar da zaben
  • Lamarin ya faru ne a Ward 1 da ke Okitipupa a jihar a yau Asabar 20 ga watan Afrilu yayin da ake shirin zaben dan takarar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Rigima ta barke a jihar Ondo yayin da ake gudanar da zaben fidda gwanin jami'yyar APC a jihar.

Lamarin faru ne a Okitipupa yayin da magoya bayan wasu 'yan takara suka kaure kan yadda ake gudanar da zaben, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ko PDP: Malamin addini ya fadi jam'iyyar da za ta lashe zabukan Edo da Ondo

An barke da rigima a zaben fidda gwanin jam'iyar APC
Wasu miyagu sun tarwatsa zaben fidda gwanin APC a jihar Ondo. Hoto: Olusola Oke, Jimoh Ibrahim, Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Mene ke faruwa a zaben fidda gwanin?

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna da za a yi a jihar a watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zabe da aka tantance sun tsere daga wurin domin tsira da rayukansu yayin da rikicin ya barke, cewar Daily Post.

Punch ta tattaro cewa rikicin ya barke ne kafin fara gudanar da zaben da kuma fara tantancewa a jihar.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa wasu daga cikin wakilan wani dan takara sun sace takardun tantancewa a mazabar.

"Daya daga cikin bakin da suka zo nan, ya sace takardun tantancewa da kuma na zaben yayin da ya tsere da motarsa."
"They bi shi amma ba su yi nasarar samunsa ba, wannan shi ne dalilin da ya jawo rikicin a wurin gudanar da zaben."

Kara karanta wannan

Kwamishinoni sun ba hammata iska a taron karbar sababbin tuba daga PDP zuwa APC

- Cewar majiyar

Fasto ya magantu kan zaben Edo da Ondo

Kun ji cewa, Shugaban cocin Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen abin da zai faru a zaben jihohin Edo da Ondo.

Ayodele ya ce akwai alamun cewa Gwamna mai ci a jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa shi ya ke da nasara a zaben.

A bangaren zaben gwamnan jihar Edo, Faston ya ce idan har ba za a yi magudi ba, to tabbas APC ce za ta yi nasara a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel