PDP Ta Samu Koma Baya Bayan Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus, an Rasa Jiga-Jigai 4

PDP Ta Samu Koma Baya Bayan Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus, an Rasa Jiga-Jigai 4

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu babban koma a jihar Imo biyo bayan ficewar wasu daga cikin manyan jiga-jiganta
  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Gerald Irona, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar inda ya dalilin cewa bai gamsu da yadda ake tafiyar da PDP ba
  • Hakazalika tsohon kakakin majalisar dokokin jihar da wasu manyan jiga-jigai uku sun raba gari da jam'iyyar adawan a jihar Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Gerald Irona, ya yi murabus a matsayin mamba na jam'iyyar PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan na cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP na baya-bayan nan waɗanda suka sanar da ficewarsu daga jam'iyyar.

PDP ta rasa mambobi a Imo
Jiga-jigan PDP na ficewa daga jam'iyyar a Imo Hoto: @officialPDPNig
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, Gerald Irona ya sanar da murabus ɗin nasa daga jam'iyyar ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta zuwa ga shugaban PDP na mazaɓar Oguta, a ƙaramar hukumar Oguta ta jihar.

Kara karanta wannan

Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gerald Irona ya bar PDP?

Tsohon mataimakin gwamnan ya danganta dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar kan rashin gamsuwa da yadda al'amura suke gudana a jam'iyyar PDP.

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Na yi takaici cewa jam'iyyar ta kauce matuƙa daga nagartattun halayen da waɗanda suka kafa ta suka ɗora ta a kai."

An rasa jiga-jigai a jam'iyyar PDP

Hakazalika, Lawman Duruji, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo, ya fice daga jam'iyyar, cewar rahoton The Street Journal.

Sauran waɗanda suka fice daga jam'iyyar adawan a jihar Imo sun haɗa da sakataren tsare-tsare na PDP a jihar, Nze Biaduo, mataimakin shugaban jam'iyyar (yankin Owerri) Pascal Uzor da jarumin masana'antar Nollywood, Charles Awurum.

Ƴan siyasan dai su ne na baya-bayan nan a ficewar da ake ta yi daga jam'iyyar PDP a jihar ta Imo.

Kara karanta wannan

Imo: Shugaban PDP ya sauka daga kujerarsa, ya fice daga jam'iyya da magoya bayansa

PDP ta yi rashi a Imo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Ihedioha wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakim kakakin majalisar wakilai, ya bayyana cewa PDP ta gaza warware matsalolinta na cikin gida ko aiwatar da dokokinta da kuma gaza yin sahihiyar adawa ga jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel