Kwanakin PDP Za Su Zo Karshe, Tsohon ɗan Majalisar Tarayya Ya Sake Ficewa

Kwanakin PDP Za Su Zo Karshe, Tsohon ɗan Majalisar Tarayya Ya Sake Ficewa

  • Yayin da rikicin PDP ke kara ƙamari, tsohon mamban Majalisar Tarayya a jihar Ebonyi ya yi murabus daga jam'iyyar
  • Hon. Sylvester Ogbaba wanda ya wakilci Abakaliki/Izzi ya sanar da yin murabus din ne a jiya Laraba 24 ga watan Afrilu
  • Ya ce ya kasance a jam'iyyar tun shekarar 1998 inda ya ce ya dauki wannan mataki ne a karan kansa bayan nazari mai zurfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - Jam'iyyar PDP ta sake shiga mummunan yanayi bayan tsohon 'dan Majalisar Tarayya ya fice daga jam'iyyar.

Hon. Sylvester Ogbaba ya yi murabus daga jam'iyyar a jiya Laraba 24 ga watan Afrilu.

Tsohon dan Majalisar Tarayya ya yi murabus daga PDP
Jami'yyar PDP ta sake shiga matsala bayan tsohon dan Majalisar Tarayya, Sylvester Ogbaba ya yi murabus. Hoto: Hon. Sylvester Ogbaba PhD.
Asali: Facebook

Yaushe Ogbaba ya sanar da barin PDP?

Kara karanta wannan

Imo: Shugaban PDP ya sauka daga kujerarsa, ya fice daga jam'iyya da magoya bayansa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon ɗan Majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogbaba ya wakilci mazabar Abakaliki/Izzi a Majalisar Tarayya a jihar Ebonyi daga shekarar 1999 zuwa 2003.

Tsohon dan majalisar ya ce ya tura takarda dauke da sanarwar murabus din zuwa shugabannin PDP a matakin jihar da karamar hukuma da gundumar Anmegu Enyigba a jihar.

Ogbaba ya kasance a PDP tun 1998

"Ina mai sanar da ku cewa a hukumance na yi murabus daga jam'iyyar PDP a wannan jihar."
"Na dauki wannan mataki ne bayan nazari mai zurfi inda fahimci yanzu lokaci ya yi da ya kamata na bar PDP."
"Na kasance a jam'iyyar PDP tun shekarar 1998 wanda na bayar da gudunmawa sosai wurin ganin jam'iyyar ta samu ci gaba."
"Wannan mataki da na dauka a karan kai na ne kuma ina godiya da dukkan goyon baya da kuma shugabanci nagari."

Kara karanta wannan

Ondo: Ƙanin tsohon gwamna ya samu tikitin takara, zai gyara jihar a shekara 1

- Sylvester Ogbaba

Jiga-jigai 8 sun watsar da PDP a Imo

A wani labarin, kun ji cewa wasu jiga-jigan PDP takwas sun yi fatali da ita inda suka fice daga jam'iyyar a jihar Imo.

Hakan bai rasa nasaba da murabus din tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha a farkon wannan mako da muke ciki.

Ihedioha wanda tsohon mataimakin kakakin Majalisar Tarayya ne ya ce PDP ta gaza yin adawa mai karfi ga jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel