PDP Ta Sake Samun Naƙasu Bayan Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus, an Rasa Jiga-jigai 8

PDP Ta Sake Samun Naƙasu Bayan Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus, an Rasa Jiga-jigai 8

  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP akalla guda takawa ne suka watsar da lema a jihar Imo a yau Laraba 24 ga watan Afrilun 2024
  • Jam'iyyar ta samu naƙasun ne bayan tsohon mataimakin kakakin Majalisar Tarayya, Emeka Ihedioha ya yi murabus
  • Emeka ya ce ya bar jam'iyyar ce saboda rashin katabus wurin yin adawa mai karfi ga jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Jami'yyar PDP ta sake cin karo da matsaloli a Imo bayan murabus din tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha.

Akalla jiga-jigan jam'iyyar PDP takwas ne suka yi murabus domin bin sahun tsohon gwamnan jihar.

Jiga-jigan PDP sun yi murabus bayan tsohon gwamna ya tsere
Kwana daya da murabus din tsohon gwamna, wasu jiga-jigan PDP 8 sun watsar da jami'yyar. Hoto: @emekaehedioha.
Asali: Twitter

Su waye suka watsar da PDP a Imo?

Kara karanta wannan

APC: Ana tangal tangal da kujerarsa, Ganduje ya fadi wadanda za su iya gyara Najeriya

Daga cikin wadanda suka yi murabus din akwai mai ba da shawara ga PDP a jihar kan shari'a, Kissinger Ikeokwu da sakataren yada labarants, Emenike Nmeregini da ma'ajin jam'iyyar, David Abanihi, a cewar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada Obioma Iheduru da Nwokeke Chukwuemeka da Stanley Okezie da sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka ba da muhimmiyar gudunmawa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka tura zuwa ga shugabannin jam'iyyar a gundumominsu da ke jihar.

Matsalolin da PDP ke fuskanta a Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta kasa ta shiga rudani kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye ta, cewar rahoton Nigerian Pilot.

Murabus din jiga-jigan jam'iyyar PDP a Imo na zuwa ne mako daya bayan gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo, tsohon gwamna ya kama gabansa

Kafin gudanar da ganawar, wasu mambobin jam'iyyar sun bukaci shugaban riko na jam'iyyar, Umar Damagun ya yi murabus daga kujerarsa.

Tsohon gwamnan PDP ya yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Emeka Ihedioha ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.

Tsohon gwamnan gwnanan jihar Imo a karkashin jam'iyyar ya bayyana murabus din nasa ne a jiya Talata 23 ga watan Afrilu.

Dan siyasar ya ce musabbabin yin murabus din nasa bai rasa nasaba da yadda jam'iyyar ta gaza yin adawa mai karfi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel