Kano: Muhuyi Magaji Ya Yi Magana Kan Fara Binciken Gwamna Abba, Ya Tabo Ganduje

Kano: Muhuyi Magaji Ya Yi Magana Kan Fara Binciken Gwamna Abba, Ya Tabo Ganduje

  • Muhuyi Magaji ya bayyana cewa mutane sun fara matsa masa lamba ya binciki gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf
  • Shugaban hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa ya ce tun Ganduje na kan kujerar gwamnan Kano ya fara gudanar da bincike a kansa
  • A ranar 17 ga watan Afrilu, 2024 ne ake sa ran za a gurfanar da shugaban APC na ƙasa a gaban babbar kotun jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, ya ce wasu mutane na kokarin tunzura shi domin ya binciki Gwamna Abba Kabir.

Magaji ya bayyana haka ne yayin da ya halarci shirin Sunrise Daily na gidan talabijin Channels ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon APC ya faɗi matakin da ya kamata Tinubu ya ɗauka a rikicin Kwankwaso da Ganduje

Abba Kabir da Muhuyi.
Muhuyi Magaji ya yi magana kan fara binciken Gwamna Abba Kabir Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jami'in ya ce ya fara binciken shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, a lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar da ke Arewa maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar yaƙi da rashawar, wanda ya jaddada cewa ya zama tilas jami'an gwamnati su kiyaye bin doka da oda, ya ce ba su matsu dole sai sun maka Ganduje a kotu ba.

PCACC za ta binciki Abba?

Da aka tambaye shi ko zai kuma binciki gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, Magaji ya ce, “Abin da mutane ke kokarin ingiza ni a kai kenan."

Magaji ya bayyana cewa ya sani sarai wasu mutane a ɓangarori daban-daban suna masa kallon mutum mai taurin kai, rahoton Naija News.

Amma a cewarsa, duk da kotu ta yanke cewa laifin satar kuɗin baitul-mali laifi ne na ƙasa amma hukumar yaƙi da rashawa ta Kano tana da haƙƙin bincikar gwamnatin Ganduje.

Kara karanta wannan

Lauya a Kano ya fadi abin da ya kamata Ganduje ya yi, ya magantu kan zargin Gwamnati

Za a gurfanar da Ganduje

A halin da ake ciki kuma, za a gurfanar da Ganduje a babbar kotun Kano ranar Laraba 17 ga Afrilu, 2024, bisa tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade.

Daga cikin laifukan da ake zargin Ganduje har da tuhumar karɓan cin hancin $413,000 da kuma N1.38bn.

Ganduje, wanda ya yi gwamnan Kano tsakanin watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023, yana fuskantar matsin lamba ya yi murabus daga mukamin shugaban APC na kasa.

PFM na zargin Kwankwaso

A wani rahoton kuma Ƙungiyar PFM ta zargi ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso da kulla maƙircin dakatar da shugaban APC.

Kungiyar wanda ke goyon bayan APC ta yi iƙirarin cewa Kwankwaso ne ya ɗauki nauyin shugabannin APC da suka dakatar da Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel