Kano: Jigon APC Ya Faɗi Matakin da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka a Rikicin Kwankwaso da Ganduje

Kano: Jigon APC Ya Faɗi Matakin da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka a Rikicin Kwankwaso da Ganduje

  • Tsohon mataimakin shugaban APC ya buƙaci Bola Tinubu ya sulhunta Kwankwaso da Ganduje domin warware rikicin siyasar Kano
  • Salihu Lukman ya ce wannan dama ce ga Tinubu da manyan jiga-jigan APC da za su jawo Kwankwaso kuma su ceto siyasar Ganduje
  • Jigon ya ce kowa ya sani Kwankwaso da NNPP suna da ƙarfi a jihar Kano don haka ya kamata Tinubu ya ɗauki matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake duba rikicin siyasar Kano.

Lukman ya buƙaci Tinubu da jagororin jam'iyyar APC su sa baki a rikicin siyasar da ke tsakanin Jagoran NNPC na ƙasa, Rabiu Kwankwaso, da shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Kano: Muhuyi Magaji ya yi magana kan fara binciken Gwamna Abba, ya taɓo Ganduje

Kwankwaso, Ganduje da Tinubu.
An nemi Tinubu ya sulhunta Ganduje da Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Ganduje, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Lukman ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon ya roƙi shugaba Tinubu ya duba abubuwa da dama a tsakaninsu baya ga zargin karɓan cin hancin $413,000 da N1.38bn, wanda gwamnatin Kano ke wa Ganduje.

Me ya haɗa Kwankwaso faɗa da Ganduje?

Tsofaffin gwamnonin Kano guda biyu, Ganduje da Kwankwaso, sun kasance abokan juna kafin su fara takun saƙa a ‘yan shekarun da suka gabata saboda sabanin siyasa.

Sai dai an wayi gari jiya Litinin da labarin dakatar da Ganduje a gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Halliru Gwanzo ne ya sanar da haka.

Gwanzo ya ce shugabannin APC na gundumar sun dauki matakin ne duba da yadda zargin cin hanci da rashawa ya rataya a wuyan Ganduje.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai ya faɗi Ministoci da Hadiman da ya kamata Tinubu ya kora daga aiki

Amma nan take APC ta jihar Kano ta soke dakatarwan tare da zargin gwamnati mai ci karkashin Abba Kabir Yusuf da ƙulla wannan makircin, rahoton Leadership.

Yadda Tinubu zai sulhunta Kwankwaso & Ganduje

Da yake mayar da martani, Lukman ya dage cewa dole ne Tinubu da manyan masu ruwa da tsaki a APC su yi gaggawar sulhunta Ganduje da Kwankwaso.

"Kasancewa masu son ci gaba yana bukatar gaskiya, kuma idan aka yi la’akari da gaskiyar siyasar da muke ciki, dole ne mu yarda cewa Sanata Rabi’u Kwankwaso da NNPP suna da ƙarfin goyon baya a jihar Kano.
"Idan har hakan na nufin sake ƙulla kawancen siyasa ko hadewa da Kwankwaso da NNPP, ya kamata shugabannin APC su yi hakan. Ya zama tilas Tinubu da APC su yi amfani da wannan damar wajen dawo da tushen goyon bayan APC.
"Babu tantama wannan dama ce ga Shugaba Tinubu ya nuna irin hazakarsa ta siyasa. Idan aka tafiyar da wannan lamari yadda ya kamata, za a iya ceto siyasar Ganduje."

Kara karanta wannan

Mambobin NNPP sun buƙaci Gwamna Yusuf na Kano ya yi murabus cikin sa'o'i 48, ta faɗi dalili

- Salihu Lukman.

Muhuyi ya magantu kan binciken Abba

A wani rahoton kuma Muhuyi Magaji ya bayyana cewa mutane sun fara matsa masa lamba ya binciki gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf.

Shugaban hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa ya ce tun Ganduje na kan kujerar gwamnan Kano ya fara gudanar da bincike a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel