Gurfanar da Ganduje da Iyalansa a Gaban Kotu, Halin da Ake Ciki a Jihar Kano

Gurfanar da Ganduje da Iyalansa a Gaban Kotu, Halin da Ake Ciki a Jihar Kano

  • An fara zaman dar dar a jihar Kano yayin da ake shirin gurdanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu
  • A ranar Laraba 17 ga watan Afrilu ne za a gurfanar da Ganduje da wasu shida ciki kuwa har da mai dakinsa, Farfesa Hafsat Umar
  • Ana tuhumar Ganduje da sauran shidan da laifin karkatar da $413,000 da kuma Naira biliyan 1.38 da suka karba a matsayin cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Da alama siyasar Kano ta dau zafi tun a karshen makon nan sakamakon fargabar da jama'a suke yi a kan shirin gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje a gaban kuliya.

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

Halin da ake ciki a Kano a kan gurfanar da Ganduje gaban kotu
Siyasar Kano ta dauki zafi yayin da za a gurdanar da Ganduje gaban kotu ranar Laraba. Hoto: @Kyusufabba, @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ganduje, wasu daga cikin iyalansa, tsofaffin mataimaka da kamfanoni, za a gurfanar da su a gaban babbar kotun jihar bisa zargin almundahana, jaridar Leadership ta ruwaito.

Tun bayan da babbar kotun jihar a ranar Talatar da ta gabata ta aike da sammaci ga tsohon gwamnan, matarsa da wasu biyar aka fara samun takun saka tsakanin 'yan siyasar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tuhumar Ganduje da almundahana

Talabijin na Channels ya ruwaito cewa Ganduje da mutane shida za su gurfanar gaban kotun a ranar Laraba 17 ga watan Afrilu bisa tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa.

Ana zargin Ganduje da karkatar da $413,000 da kuma Naira biliyan 1.38 da suka karba a matsayin kudin rashawa.

Sauran da ake tuhuma sun hada da Farfesa Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, kamfanin Lamash, kamfanin Safari da kamfanin Lesage.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

Gwamnatin jihar Kano karkashin jam'iyyar NNPP ce ta shigar da wannan karar.

An kafa kwamitin bincike a Kano

A baya bayan nan ne Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitoci biyu da za su gudanar da binciken shekaru 8 na mulkin APC a jihar.

Kwamiti na farko zai binciki badakalar sayar da kadarorin gwamnati, yayin da dayan zai binciki ta'addancin da aka yi a zabubbukan jihar daga 2015 zuwa 2023.

Sai dai gurfanar da Ganduje gaban kotu shi ne labarin da yafi karaɗe gidajen rediyo da kafofin sada zumunta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel