Lauya a Kano Ya Fadi Abin da Ya Kamata Ganduje Ya Yi, Ya Magantu Kan Zargin Gwamnati

Lauya a Kano Ya Fadi Abin da Ya Kamata Ganduje Ya Yi, Ya Magantu Kan Zargin Gwamnati

  • Yayin ake ci gaba da cece-kuce kan dakatar da Abdullahi Ganduje daga kujerarsa, wani lauya ya ba shi shawara
  • Lauyan mazaunin Kano mai suna Isa Wangida ya shawarci tsohon gwamnan jihar da ya yi murabus cikin girma har sai an kammala shari'ar
  • Hakan ya biyo bayan zargin Ganduje da badakalar kadarorin gwamnatin jihar Kano da Abba Kabir ke tuhumarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wani fitaccen lauya mazaunin Kano ya ba shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje shawara kan matsalar da ya shiga.

Lauyan mai suna Wangida Isa ya shawarci tsohon gwamnan Kano da ya yi murabus har sai bayan kammala bincike.

Kara karanta wannan

Kano: Muhuyi Magaji ya yi magana kan fara binciken Gwamna Abba, ya taɓo Ganduje

Lauya a Kano ya ba Ganduje shawara kan halin da yake ciki
Lauya a Kano, Wangida Isa ya bukaci Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga mukaminsa. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Wace shawara lauyan ya ba Ganduje?

Wangila ya ce tuhumar da ake yi kan Ganduje syna da girma kuma ya kamata ya yi murabus daga kujerarsa zuwa lokacin da zai kare kansa daga zargi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya bayyana haka ne a yau Talata 16 ga watan Afrilu a hirarsa da gidan talabijin na Channels.

Ya ce ta kamata a gurfanar da Ganduje a gaban Babbar Kotun Tarayya saboda zargin badakalar kudi da ake yi kansa mai girma ne.

Ikon APC a mazabar Ganduje

Har ila yau, lauyan ya ce shugabannin jam'iyyar a mazabar Ganduje suna da ikon dakatar da duk wani mamban jam'iyyar.

Wangida ya yi fatali da zargin cewar jam'iyyar NNPP ce ta dauki nauyin dakatar da Ganduje wurin amfani da shugabannin jam'iyyar.

Ya ce a doka yawan wadanda suka sanya hannu ya kai su dauki kowane irin mataki kan shugaban jam'iyyar ta kasa.

Kara karanta wannan

Bayan zargin Miyetti Allah kan Gwamna Sule, an dauki mataki kan ƙungiyoyin sa kai

APC ta dakatar da Ganduje a Kano

A baya, kun ji cewa jam'iyyar APC a mazabar shugaban APC ta kasa, Abdullahi Ganduje ta dauki mataki a kansa.

Jam'iyyar ta dakatar da Ganduje kan zarge-zarge da ake yi kansa na badaƙalar kudi da salwantar da kadarorin gwamnatin jihar.

Sai dai daga bisani, jam'iyyar ta karyata dakatar da Ganduje inda ta ce jam'iyyar NNPP ce ta dauki nauyin wasu domin cimma burinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel