Al’ummmar Kano Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Sharia’ar Ganduje Zata Kawo Rikici a Jihar

Al’ummmar Kano Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Sharia’ar Ganduje Zata Kawo Rikici a Jihar

  • Ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Kano sakamakon shirin gurfanar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, dakta Abdullahi Umar Ganduje
  • Jama'ar garin sun bayyana ra'ayoyinsu game da shari'ar inda wasu suke yiwa lamarin kallon bita da kullin siyasa wasu kuma suke kallon zai iya tayar da tarzoma a fadin jihar
  • Jam'iyyar adawa ta APC a jihar ta bakin shugabanta Alhaji Abdullahi Abbas, ta bayyana yadda ta dauki lamarin da matakan da zata dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yanayin siyasar jihar Kano dai na ci gaba da ɗaukan sabon salo gabanin fara binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Ganduje: APC da PDP sun rikice, shugabanninsu sun shiga garari, an gano dalili

Binciken wanda ya shafi tsohon gwamnan da iyalansa ya kawo cece-ku-ce a tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar da jam’iyyar APC.

Abba and Ganduje
Gwamnatin Kano tana zargin Ganduje ne da cin hanci da rashawa da cin amanar ofis. Hoto: Abba Kabir Yusuf/Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

An taso Abdullahi Ganduje a gaba a Kano

Binciken ya nuna cewa wata babbar kotun jihar Kano ta aika wa tsohon gwamnan da matarsa da wasu mutane shida takardar sammaci ranar Talatar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An aika sammacin ne kan zargin almundahanar kudi a lokacin da yake kan mulki, lamarin da ya kara dagula al’amuran siyasa a jihar.

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar karkashin jam’iyyar NNPP ta kafa kwamitin bincike da zai binciki shekaru takwas da gwamna Ganduje ya yi, da kuma shari’a kan zargin cin amana a ofis.

Lamarin shari'ar ya mamaye tattaunawar siyasa a gidajen rediyon jahar Kano da kafofin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa muka gayyaci Nasir El-Rufai zuwa Borno Inji Gwamnatin Zulum

Ganduje v Abba: Yadda jama'a suka kalli lamarin

Mazauna Kano da suka bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin, sun bayyana fargabar cewa rigimar da ake yi kan binciken na iya haifar da tabarbarewar tsaro a sakamakon kiyayyar da ke tsakanin bangarorin da ke rikici da juna. Ga abinda wasu mazauna Kano suka bayyanawa Legit Hausa:

Wani mazaunin Hotoro, Yakubu Isa, ya ce:

"Ina ganin wannan lokacin ba shi ne mafi kyau a haddasa yakin siyasa da juna ba, bayan haka, addini ya ce ka da a tsananta bincike."

A nasa bangaren, Tanimu Auwalu da ke Rijiyar Lemu ya bukaci gwamnan da ya mai da hankali kan harkokin mulki, inda ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta shagaltu da aiwatar da tsare-tsare a maimakon yaki da ‘yan adawar siyasa ba tare da wata bukata ba.

A nata bangaren Hajiya Ayi Isa Dosa ta yi kira ga Gwamna Yusuf da ya guji duk wani abin da zai kawo masa bata lokaci tana mai cewa masu jefa kuri'a za su duba abubuwan more rayuwa da ya kawo jihar fiye da abin da Ganduje ya yi ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Gurfanar da Ganduje da iyalansa a gaban kotu, halin da ake ciki a jihar Kano

Martanin 'yan APC kan binciken Ganduje

Garba Kore, jigo a jam’iyyar APC, a yayin da yake zantawa da gidan rediyo a Kano, ya ce matakin da gwamnan ya dauka ba dai-dai bane.

Sai dai a martanin da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi a hukumance, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ci gaba da bin doka da oda, amma ba za ta amince da farautar 'ya'yanta ba.

Bayanin 'yan sanda a kan lamarin

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ba da tabbacin samar da zaman lafiya a lokacin shari'ar, cewar jaridar Leadership

Kwamishinan ‘yan sandan, Ussaini Gumel, a wata tattaunawa ya bada tabbacin cewa jama'ar Kano na cikin aminci kuma ba wani tashin hankali da zai biyo baya.

An ja kunnen Abba a kan Ganduje

Haka zalika kun ji cewa wata ƙungiya ta yi Allah wadai da yunƙurin da gwamnatin jihar Kano ta yi na binciken tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa binciken tsohon gwamnan ba shi ba ne abin da ya damu al'ummar jihar a halin yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel