2027: Sabuwar Doka Za Ta Hana Arewa Maso Yamma da Yankin Tinubu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa

2027: Sabuwar Doka Za Ta Hana Arewa Maso Yamma da Yankin Tinubu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Da alamu Tinubu ba zai sake tsayawa takara ba yayin da ake neman dabbaka wata doka da za ta hana wasu yankuna tsayar da ‘yan takara
  • Yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Kudu za su iya rasa damar tsayar da dan takarar shugaban kasa
  • Wannan zai bai wa sauran yankunan damar tsayar da ‘yan takara wanda ba su taba samun wannan dama ba tun shekarar 1999

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Kudu za su iya rasa damar tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Wannan ya biyo bayan sabuwar doka da ke Majalisar Dokoki wacce za ta dakile yunkurin yankunan musamman a 2027.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun farmaki manoma a Borno, sun halaka mutum 3 da sace kekuna 50

Sabuwar doka za ta iya hana Tinubu tsayawa takara a shekarar 2027
Dokar za ta samar da daidaito kan tsayawa takara a wasu yankunan kasar. Hoto: House of Reps, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane sauyi dokar za ta kawo a shugabancin kasar?

Punch ta binciko cewa za a tabbatar da dokar ce don bai wa sauran yankuna damar fitar da 'yan takara kamar yadda sauran suka samu dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Majalisa mai wakiltar Apa/Agatu a jihar Benue, Ojema Ojetu shi ya gabatar da kudurin don gyaran fuska a kundin tsarin mulki.

Dokar idan ta tabbata za ta dakile yankunan wurin tsayar da dan takara wanda suke yi tun bayan dawowar dimukradiyya a shekarar 1999.

Har ila yau, dokar ta na neman bai wa yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Gabas damar tsayar da ‘yan takara.

Sauran sauye-sauye game da sabuwar dokar

Cewar dokar:

“Duk yankin da ya samar da shugaban kasa ba zai sake samun damar ba har sai sauran yankunan sun samar da na su shugaban.”

Kara karanta wannan

An karrama sojoji 8 da suka ƙi karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga hannun ɓarayin shanu

Wannan zai bai wa sauran yankunan uku damar samun shugaban kasa wanda ba su taba samu ba tun a shekarar 1999.

Dadi da kari, gwamnonin jihohi ma dole za su bi tsarin inda ko wane yanki ko mazabar Tarayya za ta samu damar fitar da dan takarar gwamna, 9News Nigeria ta tattaro.

Har ila yau, a bangaren sanatoci ma dole ko wane yanki a mazabar a ba shi damar tsayar da dan takarar sanata ba tare da tauye hakki ba, cewar Spectacle.

Majalisa ta ayyana Kogi cikin masu arzikin mai

Kun ji cewa Majalisar Tarayya ta ayyana jihar Kogi a matsayin daya daga cikin jihohin Najeriya masu arzikin man fetur.

Hakan ya biyo bayan zazzafar muhawara da aka yi kan kudurin inda aka tabbatar da jihar daga cikinsu da kuma samun kaso 13 na kudaden man.

Asali: Legit.ng

Online view pixel