Idan Kayi Wannan, Ka Ci Zaben 2027 Ka Gama, Jigon PDP Ya Ba Tinubu Lakanin Tazarce

Idan Kayi Wannan, Ka Ci Zaben 2027 Ka Gama, Jigon PDP Ya Ba Tinubu Lakanin Tazarce

  • Idan Bola Ahmed Tinubu ya cika alkawarin APC na canza fasalin Najeriya, zai zarce idan ya tsaya takara
  • Ra’ayin Reno Omokri shi ne jam’iyyar APC za ta sake yin galaba a zaben 2027 idan ta iya yin wannan aiki
  • Fasto Omokri ya ce idan Tinubu ya gaza a fannin nan, al’umma za su ba Atiku Abubakar kuri’unsu a 2027

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Idan gwamnatin Bola Tinubu za ta iya sauya tsarin mulki da fasalin kasa nan da 2027, Reno Omokri bai hango nasara.

Fasto Reno Omokri wanda yana cikin fitattun ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, har ya fara hasashe zabe mai zuwa da za ayi a farkon 2027.

Atiku Tinubu
Bola Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: @officialABAT, @Atiku
Asali: Twitter

Reno Omokri ya yi magana a dandalin X, ya ce muddin gwamnatin APC ta sauya fasalin kasa, za ta zarce a mulki har 2031.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gamu da rudanin takarar farko a APC tun bayan zama shugaban jam’iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me za su taimaki Tinubu a 2027?

Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya ce bayan sauya fasalin mulki, kirkiro ‘yan sandan jihohi zai ba APC damar zarcewa.

Idan kuwa Bola Tinubu ya gagara yin wadannan, Omokri ya ce jama’a za su goyi bayan Wazirin Adamawa watau Atiku Abubakar.

Peter Obi zai kashe Atiku

Sharadin nasarar Atiku a wurin Omokri shi ne rashin tsayawa takarar Peter Obi.

Idan ‘dan takaran LP a zaben shekarar bara ya nemi mulkin Najeriya, Omokri yana ganin Atiku da jam’iyyar PDP sun gama yawo.

Masana da masu fashin baki sun gamsu cewa raba kuri’un adawa da Peter Obi ya yi a zaben 2023 ya taimakawa APC da Tinubu.

An dade ana kukan ya kama jihohi su samar da jami’an ‘yan sanda domin inganta tsaro.

Maganar Reno Omokri a kan 2027

Kara karanta wannan

Ganduje da dalilai 5 da suka yaudari APC, a karshe Abba ya tsare kujerarsa a Kotun Koli

"Idan Tinubu zai samar da tsarin tarayya na hakika da ‘yan sandan jihohi, babu abin da za hana shi sake cin zabe a 2027.
Idan ya gaza samar da wadannan, mutanen Najeriya za su koma goyon bayan Wazirin Adamawa, Atiku a shekarar 2027.
Kuma muddin Obi bai sake yin takara ba, Waziri zai iya ci. Amma idan Peter Obi ya shiga takara a 2027, za a yi irin na 2023."

- Reno Omokri

Ana rigimar cikin gida a APC

Jam'iyyar APC ta shirya zaben shiga takarar majalisa, amma hatsaniya ta biyo baya a Ondo, an ji labari batun ya kai gaban majalisar NWC.

Olugbenga Araoyinbo ya fadawa APC-NWC ta soke takarar Ifeoluwa Ehindero, ayi sabon zabe domin maye kujerar Olabunmi Tunji-Ojo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel