2023: Bola Tinubu Ya Ambato Mutum 2 da Suka Hana Atiku Zama Shugaban Najeriya

2023: Bola Tinubu Ya Ambato Mutum 2 da Suka Hana Atiku Zama Shugaban Najeriya

  • Lauyan da yake kare Bola Tinubu a kotun karar zabe ya yi wa Atiku Abubakar da Lauyoyinsa raddi
  • ‘Dan takarar na Jam’iyyar APC ya ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka daukewa PDP kuri’unta
  • LP da NNPP sun samu kuri’u 6,101,533 da 1,496,687 a zaben shugaban kasa, amma ba suyi masu amfani ba

Abuja - Bola Tinubu da ya lashe zaben sabon shugaban kasa da aka yi a bana, ya yi bayanin abin da ya hana Atiku Abubakar kai labari a jam’iyyar PDP.

Punch ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya nuna babu ta yadda Alhaji Atiku Abubakar zai yi galaba a kan shi domin sauran ‘yan adawa sun raba kuri’unsu a zaben.

‘Dan takaran na APC ya fadawa kotun sauraron korafin zaben 2023 cewa kuri’un da ya kamata PDP ta samu, sun kare a hannun jam’iyyun NNPP da LP.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Na Tika Ka da Kasa a Takarar Shugaban Najeriya – Bola Tinubu ga Peter Obi

Lauyoyin Tinubu su ka ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da suka nemi mulki a wannan karo duk su na tare da jam’iyyar PDP a zaben da aka yi a baya.

LP da NNPP suka kashe PDP?

Ko da Tinubu da Atiku sun samu kuri’u 8,794,726 da 6,984,520 ne kamar yadda INEC ta sanar, mutum 6,101,533 da 1,496,687 suka zabi Obi da Kwankwaso.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyoyin Atiku Abubakar sun kai korafi, su na rokon a soke nasarar da hukumar INEC ta ba APC, suka ce ba Tinubu ya dace ya zama zababben shugaba ba.

Tinubu and Atiku
Bola Tinubu da a Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

The Nation ya ce hakan ta sa Tinubu ya yi hayar Lauyoyi domin kare shi. Wajen bada kariyar ne suka ce barin PDP da wasu suka yi, shi ya hana ta galaba.

A cewar Lauyan da yake bada kariya ga zababben shugaban na Najeriya, jam’iyyar PDP ta fi karfi a lokacin da Atiku ya yi takara da Buhari a zaben 2019.

Kara karanta wannan

Jerin Yan Takarar Shugaban Kasa Da Jam’iyyun Da Ke So Kotu Ta Tsige Tinubu a Matsayin Zababben Shugaban Kasa

Dalilinsa shi ne a wancan lokaci, Peter Obi ya tsaya a matsayin abokin gamin Wazirin Adamawa, sannan magoya bayan Kwankwaso sun goyi bayan PDP.

Bayan shekaru hudu, babbar jam’iyyar hamayyar ta rasa wadannan mutane biyu wadanda bayan sun sauya-sheka, su ka gwagwiyi miliyoyin kuri’un.

Dalilin doke LP - Tinubu

Wazirin Adamawa yana sa ran kotu ta hana a rantsar da Tinubu, wannan ne rokon jam’iyyar LP, amma Rabiu Kwankwaso da NNPP ba su kai je kotu ba.

A jiya aka ji Bola Tinubu ya fadawa Peter Obi cewa ba a san shi da tsalle-tsallen canza sheka ba, ya kuma ce kafuwar da ya yi a kasa, ta ci masa zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel