Abba Ya Nunawa Duniya Masoyansa a Kano da Ya Dawo Bayan Hukuncin Kotun Koli

Abba Ya Nunawa Duniya Masoyansa a Kano da Ya Dawo Bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Dubban daruruwan masoya da magoya baya suka tarbi Abba Kabir Yusuf da ya dawo jihar Kano a jiya
  • Gwamnan ya samu kyakkyawan lale maraba daga jama’a bayan yin galabar shari’ar zabe a kotun koli
  • Abba ya shafe awanni yana gaida ‘Yan Kwankwasiyya da masu kaunarsa daga Kaduna zuwa jihar Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Dubban masoya, magoya baya da ‘yan jam’iyyar NNPP su ka tarbi Abba Kabir Yusuf da ya dawo jihar Kano a ranar Lahadi.

An bada sanarwar za a tarbo Mai girma gwamnan Kano a Chiromawa da karfe 11:00 na safe, amma sai cikin dare ya iso Filin mahaha.

Abba.
Abba Gida Gida a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Tafiyar Abba daga Kaduna zuwa Kano

Legit ta hausa ta bibiyi yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya taso tun daga garin Kaduna bayan hukuncin kotun koli zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a garin Kaduna da birnin Zazzau gwamnan na Kano ya rika cin karo da masoya da su ka taya shi murnar yin nasara a kan APC.

Dinbin mutane sun tare motar gwamnan a garin Tashar Yari, haka ya yi ta cin karo da jama’a har zuwa karamar hukumar Kura a Kano.

Daga Karfi zuwa Kwanar Dangora, wani hadimin gwamnan ya ce sai da su ka shafe awanni biyu suna cin karo da tarin al'umma.

Jihar Kano ta cika ta batse domin Abba

Jama’a sun ga taron da ba a saba gani ba a lokacin da Abba Gida Gida zai wuce ta Na’ibawa, masoya sun cika gadar ‘yan lemu.

Zuwa lokacin da gwamna Abba ya iso tashar unguwa uku da kimanin karfe 7:00, rana ta fada, bai isa gadar Lado bai sai kusan 8:00.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

Gwamnan Kano a Filin Mahaha

Gwamnan ya bi ta hanyar jami’ar Bayero zuwa filin mahaha, inda a nan aka yi masa tarba ta musamman da kimanin karfe 10:00 na dare.

Babban mai taimakawa gwamna kafofin zamani, Abdullahi Ibrahim ya wallafa cewa Abba ya iso gida a fadar gwamnati da kusan karfe 12:00.

Jama’a suka yi wa gwamnan rakiya yayin da ake murna da cashewar yin galaba kan Nasiru Gawuna da APC a kotun koli a makon jiya.

"Mun ga jama'a kamar hauka" inji wani Bakano

Legit ta zanta da wani mazaunin Na’ibawa wanda ya ce tun karfe 2:00 na rana suka fito, amma ba su dawo gida bai sai lokacin Isha’i.

Sulaiman Shehu ya fada mana rabon da ya ga taron mutane irin haka tun lokacin da Rabiu Kwankwaso ya sake takarar gwamna a 2011.

Majiyoyinmu sun shaida mana ba a bar mata a baya wajen fitowa ganin Abba ba, mutane sun fita da iyalinsu domin tarbo gwamnan.

Kara karanta wannan

Da an hana Abba Gida-Gida mulkin Kano, da Najeriya ta kama da wuta, inji Buba Galadima

Abba ya fallasa shirin Ganduje a Kotun koli

An samu labari ana zargin Abdullahi Umar Ganduje ya nemi ya kebe da Bola Tinubu kafin hukuncin zaben gwamnan Kano a kotun koli.

Zaman shugaban kasa da shugaban na APC ba ta yiwu ba, a karshe NNPP ta rike mulkin Kano, lamarin da jam’iyyar APC ba ta ji dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel