Kotun Koli Ta Fara Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Kotun Koli Ta Fara Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

  • A zaman da ta yi na sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe
  • A hukuncin da Kotun ta yanke, ta tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP shi ne halastaccen gwamnan Kano
  • Kotun Koli ta ce Kotun Daukaka Kara da ta kararrakin zabe sun yi kuskure wajen tsige Abba daga gwamnan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kotun Koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a 2023.

Tun da fari Gwamna Yusuf ya nemi Kotun Kolin da ta yi watsi da hukuncin da kotun kotun daukaka kara da na kotun kararrakin zabe da suka tsige shi daga gwamna.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar Abba Gida-Gida da Gawuna.
Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar Abba Gida-Gida da Gawuna. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Abba Kabir ne halastaccen gwamnan Kano - Kotu

A hukuncin da Kotun ta yanke, ta ce Kotun Daukaka Kara da kotun kararrakin zabe sun yi kuskure wajen korar Abba daga kujerar gwamnan Kano, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun dai tun da fari ta fara ajiye batu kan yanke hukuncin shari'ar a ranar 21 ga watan Disamba 2023.

A watan Satumba, kotun kararrakin zabe ta kori Abba Kabir Yusuf daga gwamnan Kano, jaridar The Cable ta ruwaito.

A watan Nuwamba kuma Kotun Daukaka Kara ta kara tabbatar da korar Abba daga kujerar gwamnan.

Duka kotunan biyu, sun bayyana Nasiru Gawuna da jam'iyyar APC matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Bauchi: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala

A zaman da ta yi a ranar Juma'a, Kotun Koli ta yanke hukuncin karshen kan shari'ar zaben gwamnan jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Yadda Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba a kan Gawuna da APC a zaben Kano

A hukuncin da ta yanke, kotun ya kori karar da Abubakar Sadique na APC ya shigar, tare da tabbatar da nasarar Bala Mohammed matsayin gwamnan Bauchi.

Hotunan Abba Gida-Gida yana murnar samun nasara a Kotun Koli

A wani labarin, Legit Hausa ta wallafa wasu hotuna da ta ci karo da su na gwamna Abba Kabir Yusuf bayan samun nasara a Kotun Koli a ranar Juma'a.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon hukuncin kotun, halastaccen gwamnan Kano Abba, ya wallafa jawabin godiya ga Allah a Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel