Yanzun Nan: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

Yanzun Nan: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

  • Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta raba gardama kan sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano
  • A ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023, Kotun ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ta kuma yanke cewa Abba ba ɗan jam'iyyar NNPP bane lokacin da aka ba shi takara, don haka haramun ne ya shiga zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Nasiru Yusuf Gawuna da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Yanzun Nan: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano Hoto: Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwamitin alkalan kotun ya tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya umurci a bai wa Emefiele masauki a gidan yarin Kuje

Idan baku manta ba, Kotun sauraron kararakin zaɓe ta bayyana kuri'u 165,663, daga cikin kuri'un da Gwamna Yusuf ya samu a matsayin haramtatun kuri'u.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙaramar Kotun ta soke waɗan nan kuri'u ne bisa hujjar cewa ba su inganta ba saboda babu satanfi da sa hannun hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a jikinsu.

Daga nan sai ta rage kuri’un gwamnan zuwa 853,939 yayin da na Nasir Ganuwa, abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ke da kuri'u 890,705.

Nasiru Gawuna ne zababben Gwamnan Kano - Kotu

Bayan haka ne Kotun ta bayyana Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da ƙuri'u mafi rinjaye, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamna Yusuf ya ki amincewa da hukuncin kotun, wanda ya bayyana a matsayin "rashin adalci," inda ya garzaya kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Tinubu ya shiga babbar matsala kan tsige Gwamna Abba Gida-Gida

Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023, Kotun ɗaukakaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke na tsige Abba.

Ta kuma yanke hukuncin cewa tsaida Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar NNPP ya saɓa wa doka domin bai cancanci ya tsaya takara ba saboda ba ɗan jam'iyya bane.

An matsawa Tinubu lamba kan shari'ar zaben gwamnan Kano

A wani rahoton kuma Ƙungiyoyi da wasu jagororin siyasa sun gargaɗi shugaban kasa, Bola Tinubu, ya guji neman tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Wata kungiya mai rajin kawo ci gaba ta yi gargaɗin cewa sauke gwamnan daga mulki ka iya tarwatsa siyasa da haɗin kan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel