Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tsige Gwamnan APC, Ta Fadi Dalilai

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tsige Gwamnan APC, Ta Fadi Dalilai

  • Kotun Koli da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Ebonyi
  • Kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da ke neman tsige Gwamna Francis Nwifuru na jami'yyar APC
  • A baya Kotun Daukaka Kara ta yi fatali da karar dan takarar PDP a jihar, Chukwuma Odii saboda rashin hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar neman tsige Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.

Mai Shari'a, John Okoro shi ya tanadi hukuncin bayan dukkan bangarorin sun gabatar da korafe-korafensu, cewar Channels TV.

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Ebonyi. Hoto: Francis Nwifuru.
Asali: Twitter

Wane mataki kotun ta dauka a yau?

Okoro ya ce za su tuntube su kan lokacin da za a sanar da hukuncin karshe kan shari'ar ta su da ake yi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Jerin ƙararraki 21 da kotun koli zata saurara da yanke hukunci kan zaben wasu gwamnoni a mako 1 tal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC.

Kotun da ke zamanta a Legas, ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odii saboda rashin hujjoji.

Alkalin kotun ya ce Odii ba shi da hurumin shiga harkar jami'yyar APC kan zaben fidda gwani kafin babban zabe.

Wane hukunci kotun ta yanke a Benue?

Har ila yau, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue wanda ke jami'yyar APC, cewar Punch.

Kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP a jihar, Titus Uba saboda rashin gamsassun hujjoji.

Titus na kalubalantar zaben ne saboda zargin tafka mummunan magudi a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Watakila a yanke hukuncin zaben Kano ranar Juma'a

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukuncin karshe kan manyan gwamnonin APC 2, ta yi bayani

A wani labarin, Akwai alamun cewa Kotun Koli za ta yanke hukuncin zaben jihar Kano a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar, Nasiru Gawuna shi ke kalubalantar zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

A kwanakin baya dai Kotun Kolin ta tanadi hukunci kan shari'ar da ta dauke hankulan mutane da dama a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel