Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Karshe Kan Manyan Gwamnonin APC 2, Ta Yi Bayani

Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Karshe Kan Manyan Gwamnonin APC 2, Ta Yi Bayani

  • Kotun Koli ta shirya yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnonin jihohin Benue da Ebonyi a yau Litinin
  • Dan takarar jam'iyyar PDP a Benue, Titus Uba na kalubalantar zaben Gwamna Alia Hyacinth na APC
  • A Ebonyi kuwa, dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odii na kalubalantar zaben Gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta shirya raba gardama a shari'ar zaben gwamnonin jihohin Benue da Ebonyi.

Mai Shari'a, John Okoro shi zai jagoranci alkalan biyar a yau Litinin 8 ga watan Janairu a Abuja.

Kotun Koli ta sanya ranar raba gardama kan shari'ar gwamnonin APC 2
Kotun Koli za ya yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnonin Benue da Ebonyi. Hoto: Alia Hyacinth, Francis Nwifuru.
Asali: Facebook

Yaushe za a yanke hukuncin a Benue da Ebonyi?

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia da mataimakinsa, Sam Ode sun halarci sauraran shari'ar a a yau, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Jerin ƙararraki 21 da kotun koli zata saurara da yanke hukunci kan zaben wasu gwamnoni a mako 1 tal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar, Titus Uba shi ke kalubalantar zaben Gwamna Alia na jam'iyyar APC.

Kotun Daukaka Kara a kwanakin baya ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Wane hukunci kotun ta yanke a baya?

Kotun ta ce babu wani hurumin sauraran korafe-korafen da takarar jam'iyyar PDP saboda matsala ce ta kafin zabe, cewar Politics Nigeria.

Har ila yau, ta ce ya kamata Uba ya kalubalanci takardun bogi da ya ke zargi kan mataimakin gwamna, Sam Ode a babbar kotu.

A jihar Ebonyi kuwa, Kotun Daukaka Kara da ke jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru a matsayin gwamnan jihar.

Yayin hukuncin kotun, alkalan kotun sun yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odii saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar neman tsige gwamnan APC, ta fadi dalilai

Ta yiyu a yanke hukunci a shari'ar Kano a wannan mako

A wani labarin, Akwai alamun cewa Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu.

Dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Nasiru Gawuna shi ke kalubalantar zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

Har ila yau, a ranar ta Juma'a watakila a yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau da ake ta cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel