An Zargi Abba Gida Gida da Nada Mutum 3 a Duk Karamar Hukuma Domin 'Karya' APC

An Zargi Abba Gida Gida da Nada Mutum 3 a Duk Karamar Hukuma Domin 'Karya' APC

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada jami’ai uku da za su yi aiki a kowace karamar hukumar a jihar Kano
  • Wasu sun ce ba komai ya sa aka yi hakan ba sai saboda a yaki shugabannin kananan hukumomin jihar
  • Babu yadda Mai girma Abba Yusuf zai yi da shugabannin da aka zaba, watakila shiyasa ya tura mutanesa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Nadin wasu mukamai da Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi kwanan nan, ya jawo ana ta korafi da surutai a jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada jami’ai uku a kowace karamar hukuma, Daily Trust ta ce hakan bai kwantawa wasu a rai ba.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Gida Gida da Nasiru Gawuna Hoto: Abba Kabir Yusuf, Journalist KC
Asali: Twitter

Wadannan ma’aikata za su zama sila, da su ne gwamnatin jiha za ta rika tattaunawa da ma’aikatan kananan hukumomi a Kano.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Kada ku cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan Kano - Shugabannin Hausawa a kudu

APC ta bar Abba da ala-ka-kai a Kano

Wasu suna zargin cewa an nada su ne domin taka shugabannin kananan hukumomin da ke kan mulki wadanda ‘yan APC ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dokar kasa, gwamna bai da hurumin tsige shugabannin kananan hukumomin domin jama’a ne su ka kawo su ta hanyar yin zabe.

Martanin jam'iyyar APC

Sakataren APC na jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina ya ce wadannan jami’ai da aka nada ba su da hurumi da gindin zama a dokar kasa.

Alhaji Ibrahim Zakari Sarina yana ganin ba su da ikon kawowa shugabannin kananan hukumomi tasgaro wajen gudanar da aikinsu.

...Aikin Abba bai ci karo da doka ba - Lauya

Amma lauyoyi irinsu Abba Hikima sun shaidawa jaridar nadin bai sabawa doka ba.

Muddin gwamnati za ta ba su aikin da za su yi a ofis, fitaccen lauyan mai kare hakkin mutane yana ganin Abba Yusuf bai yi laifi ba.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Meyasa gwamnatin Kano ta nada su?

Sakataren yada labaran mataimakin gwamnan Kano, Ibrahim Garba Shu’aibu, ya yi karin haske game da jami’an nan da aka nada.

Alhaji Ibrahim Shu’aibu ya ce makasudin nadin su yi aiki tare da shugabannin kananan hukumomi, ba su kalubalance su ba.

Abba zai cigaba da mulkin Kano?

A makon jiya aka samu rahoto cewa malaman musulunci sun yi addu’a domin Alkalan kotun koli su tabbatar da mulkin NNPP.

An gargadi Bola Tinubu cewa ka da ya tsoma baki a shari’ar da ake yi a kan zaben gwamnan jihar Kano tsakanin Abba Yusuf da APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel