Zaben kananan hukumomin Kano: Zamu lashe dukkan kujeru 44, Ganduje ya bayyana

Zaben kananan hukumomin Kano: Zamu lashe dukkan kujeru 44, Ganduje ya bayyana

- Yau Asabar, 16 ga Junairu, ana gudanar da zaben kananan hukumomin Kano

- Ganduje, Gawuna, Alibaba, da sauran jigogin APC sun kada kuri'unsu a kauyukansu

- Tuni da am'iyyar PDP ta ce zata kauracewa da zaben

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi hasashen cewa jam'iyyarsa ta All Progressive Congress (APC) za ta lashe zaben dukkan kananan hukumomi 44 da gunduma-gunduma 484 dake jihar.

Ganduje ya ce ya yi hasashen haka ne bisa yadda ya ga mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu, rahoton Daily Trust.

Yayin jawabi bayan kada kuri'arsa a kauyensa na Ganduje, ya ce ana zaben cikin zaman lafiya da lumana.

"Wannan na nuna cewa dukkan mutan jihar Kano sun amince da zaben," Ganduje ya bayyana.

"Wannan na kara mana karfin gwiwa musamman saboda bamu yarda kwamitocin rikon kwarya su cigaba da mulkin kananan hukumomi ba, saboda haka wajibi ne a zabi shugabanni don jagorantan lamarin kananan hukumominmu 44."

"Kamar yadda kuke gani, mutane na natse, suna kada kuri'unsu. Babu tsangwama, babu wanda aka ciwa mutunci kuma mutane na kada kuri'arsu yadda suke so."

"Abinda muke zato shine zamu lashe sukkan kananan hukumomin 44 wanda ya hada kujerun shugabanni 44 da kansililo 484," Ganduje ya kara.

Ya yi kira ga masu zabe su kada kuri'arsu yayinda yake tabbatar musu cewa wadanda aka zaba zasu yi musu aiki.

KU KARANTA: Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla

Zaben kananan hukumomin Kano: Zamu lashe dukkan kujeru 44, Ganduje ya bayyana
Zaben kananan hukumomin Kano: Zamu lashe dukkan kujeru 44, Ganduje ya bayyana Hoto: Ganduje TV
Source: Facebook

KU DUBA: Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo

Gabanin zaben yau, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar (KANSIEC) a ranar Laraba ta ce tayi watsi da yan takara shida saboda sun kasa tsallake gwajin kwayoyi.

Daily Trust ta ruwaito KANSIEC ta ce da kirkiri gwajin kwayoyi kuma wajibi ne ga duk dan takarar da ke son neman kujerar shugaban karamar hukuma ko kansila a zabe me zuwa saboda yawaitar shaye shaye a jihar.

Shugaban hukumar, Prof Garba Ibrahim Sheka, wanda ya tabbatar da batun yayin da yake zantawa da yan jarida akan shirye shiryen da hukumar ke yi na zaben.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel