Kotun Zabe Ta Yi Watsi Da Bukatar Gwamna Sani a Kan Karar PDP Da Ashiru

Kotun Zabe Ta Yi Watsi Da Bukatar Gwamna Sani a Kan Karar PDP Da Ashiru

  • Kotun zabe ta yi watsi da karar farko da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya shigar a kan dan takarar PDP, Isah Mohammed Ashiru
  • Tawagar lauyoyin Sani ta shigar da kara cewa PDP da Ashiru sun shigar da kara bayan kwana 21 da doka ta yarda da shi
  • Kotun zabe ta bayyana cewa PDP da Ashiru sun shigar da kara a ranar 10 ga watan Afrilun 2023, don haka ta yi watsi da bukatar Gwamna Sani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Kaduna ta yi watsi da karar farko da Gwamna Uba Sani ya shigar kan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Gwamna Sani ya gabatar da bukatar ne a kan lokacin da aka shigar da karar, yana mai cewa masu karar sun shigar da ita ne bayan kwanaki 21 da doka ta ba su.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

Kotun zabe ta fara yanke hukunci kan zaben gwamnan Kaduna
Kotun Zabe Ta Yi Watsi Da Bukatar Gwamna Sani a Kan Karar PDP Da Ashiru Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Kotun zabe ta yi watsi da bukatar Gwamna Sani

Sai dai kuma, kwamitin mutum uku na kotun zaben karkashin jagorancin Mai shari'a Victor Oviawe, ta tabbatar da cewar an shigar da karar ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka, kotun zaben ta yi watsi da karar Gwamna Sani.

Fargaba yayin da kotun zabe za ta yanke hukuncin zaben gwamnan Kaduna ta manhajar Zoom

Da farko mun ji cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke Kaduna ta yanke shawarar gabatar da shari'ar ta manhajar 'Zoom'.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Isa Ashiru na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris.

Kotun ta samar da kayayyaki don tabbatar da gudanar da shari'ar ta 'Zoom' a cikin kotun.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

APC ta tsure da PDP ta kawo hujjoji a kotu domin karbe kujerar gwamnan Kaduna

A baya, mun ji cewa Gwamna Uba Sani bai yi na'ad hujjojin da ake yunkurin amfani da su daga hukumar zabe a gaban kotun zaben shi ba.

Hakazalika, Uba Sani yana son kotun zaben ta yi fatali da karar da PDP ta kai gabanta na kalubalantar nasararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel