Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam’iyyar APGA Kan Gwamnan APC

Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam’iyyar APGA Kan Gwamnan APC

  • Kotun zaben gwamnan jihar Ebonyi ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar APGA da dan takararta suka shigar gabanta dangane da nasarar Gwamna Francis Nwifuru
  • Kotu ta yi watsi da karar da ke kalubalantar nasarar gwamnan na jam'iyyar APC
  • Ta ce gaba jam'iyyar APGA da dan takararta, Bernard Odoh basu da hurumi a cikin karar da suka shigar don haka ta yi watsi da shi

Jihar Ebonyi - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ebonyi ta yanke hukunci a kan karar da jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) da dan takararta a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Bernard Odoh suka shigar a kan Gwamna Francis Nwifuru.

APGA da Odoh sun shigar da kararraki suna masu kalubalantar nasarar Gwamna Nwifuru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.

Kara karanta wannan

APC Ta Samu Nasara, Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna a Zaben 2023

Kotun zabe ta yi watsi da karar APGA kan gwamnan Ebonyi
Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam’iyyar APGA Kan Gwamnan APC Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Twitter

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Nwifuru na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, rahoton Punch.

Kotu ta yi watsi da karar APGA kan nasarar gwamnan Ebonyi

Odoh ya yi korafi ta hannun lauyansa, Jibrin Okutepa, SAN, cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Nwifuru wanda ya kasance dan majalisar wakilan jihar Ebonyi kuma kakakin majalisar jihar a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party har zuwa lokacin zaben bai cancanci tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Ebonyi ba."

Sakamakon haka, APGA da Odoh sun bukaci kotun da ta soke nasarar Mista Nwifuru saboda rashin cancantarsa ​​a zaben.

Sai dai kuma, da yake zartar da hukunci, kwamitin kotun zaben mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a Lekan Ogunmoye, ya riki cewa masu karar basu da hurumin shigar da karar saboda lamarin na cikin gida ne na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Jam'iyyar ADC Bisa Nasarar Gwamnan Jihar Gombe

Kotun ta bayyana cewa gaba daya bukatun da APGA da dan takararta suka gabatar ya fada ne kan lamuran da suka shafi kafin zabe sannan ta yi watsi da ikirarin masu karar, rahoton The Nation.

INEC ta nuna damuwa kan yanayin tsaro a jihohin Kogi da Imo gabanin zaben gwamna

A wani labarin, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta nuna damuwa matuƙa dangane da yanayin matsalar tsaro a jihohin Kogi da Imo.

Hukumar ta bayyana damuwa kan lamarin ne yayin da take shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni a jihohin guda biyu nan da 'yan watanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng