Ebonyi: Gwamna Nwifuru Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Zabe
- Gwamnan jihar Ebonyi ya buƙaci abokan takararsa a zaɓen gwamnan jihar da su zo a haɗa kai da su wajen ciyar da jihar gaba
- Gwamnan ya buƙaci hakan ne bayan nasarar da ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar ta yi fatali da ƙarar da abokan takararsa suka shigar suna ƙalubalantar nasararsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya buƙaci abokan takararsa a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, da su ba shi haɗin kai wajen ciyar da jihar gaba.
Gwamna Nwifuru ya buƙaci abokan takarar nasa da su kawo duk shirye-shiryen da suke da su domin a bunƙasa cigaban jihar, cewar rahoton Daily Post ta tabbatar.
Jaridar PM News ta ce Nwifuru ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, a birnin Abakaliki babban birnin jihar, lokacin da yake martani kan nasarar da ya samu a kotun zaɓe.
Kotun zaɓen dai ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar da Nwifuru ya samu a zaɓen gwamnan da aka yi na ranar 18 ga Maris 2023, wacce ɗan takarar jam'iyyar PDP, Dr Ifeanyichukwu Odii ya shigar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Farfesa Bernard Odoh ya shigar, inda ta ce dukkansu ba su cancanta ba.
Wacce buƙata Nwifuru ya nema wajen ƴan adawa?
A kalamansa:
"Na tuntuɓi abokan takara ta bayan na yi nasara a zaɓe domin su haɗa kai da ni wajen bunƙasa jihar amma sai suka tunkari kotu domin neman haƙƙinsu."
Cikin Gwamnan APC Ya Duri Ruwa, Kotu Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Sahihanci Nasararsa a Zabe
"Har yanzu ina kira gare su da su kawo ra'ayoyin da suke da su domin mu ciyar da jihar nan gaba."
Gwamnan Legas Ya Magantu Bayan Nasararsa a Kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Legas na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Babajide Sanwo-Olu, ya yi maraba da hukuncin da kotun zaɓen gwamnan jihar ta yanke.
Sanwo-Olu ya bayyana hukuncin kotun wanda ya tabbatar da nasarasa a matsayin na kowa da kowa, inda ya buƙaci al'ummar Legas da su ba shi haɗin kai wajen ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng