Kotu Ta Tabbatar Da Sahihancin Zaben Gwamna Nwifuru Na Jihar Ebonyi

Kotu Ta Tabbatar Da Sahihancin Zaben Gwamna Nwifuru Na Jihar Ebonyi

  • Kotun sauraron zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta raba gardama kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar da ake yi a gabanta
  • Kotun ta tabbatar da nasarar da gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar All Ptogressives Congress (APC) ya samu a zaɓen gwamnan jihar
  • Kotun wacce ke da alƙalai uku ta yi fatali da ƙararrakin da jam'iyyun PDP da APGA suka shigar a gabanta saboda rashin cancanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ebonyi - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da nasarar gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen gwamnan jihar.

Kotun ta bayyyana gwamna Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris 2023, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Nwifuru
Kotun ta tabbatar da sahihancin zaben gwamna Francis Nwifuru Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Nwifuru, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu ƙuri'u 199,131 inda ya doke Ifeanyi Odii na jam'iyyar PDP wanda ya samu ƙuri'u 80,191.

Bernard Odoh, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ya zo na uku da ƙuri'u 52,189.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a A. Ogunmoye, ta yi watsi da ƙararrakin da jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Cif Ifeanyi Odii, suka shigar kan gwamna Nwifuru da ƙarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), da ɗan takararta, Farfesa Benard Odoh.

A cewar kotun, waɗanda suka shigar da ƙarar sun kasa tabbatar da zargin da suke yi na cewa gwamna Nwifuru bai samu ƙuri'u mafiya rinjaye da aka kaɗa a lokacin zaɓen ba, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Alƙalan sun bayyana cewa masu shigar da ƙara sun kasa tabbatar da cewa Nwifuru har yanzu ɗan jam'iyyar PDP ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamna a zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

APC Ta Samu Nasara, Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna a Zaben 2023

Sakamakon hakan sai kotun ta kori ƙararrakin saboda rashin cancanta.

Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Sokoto

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta sanya ranar Asabar, 30 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.

Jam'iyyar PDP da ɗan takararta Saidu Umar, na ƙalubalantar nasarar da gwamna Ahmed Aliyu ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel