Zamani Ya Juyo da Mataimakin Gwamna Ya Koma Sakataren Gwamnati Bayan Shekaru

Zamani Ya Juyo da Mataimakin Gwamna Ya Koma Sakataren Gwamnati Bayan Shekaru

  • Gwamnan jihar Katsina ya zabo wanda zai zama sabon Sakataren gwamnati bayan canjin da aka yi
  • Dikko Umaru Radda ya dawo da tsohon Mataimakin Gwamna, Abdullahi Garba Faskari ya zama SGS
  • Abdullahi Garba Faskari zai maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa wanda yake shirin zama Ministan kasa

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin Abdullahi Garba Faskari a matsayin sakataren gwamnatin jiha.

Babban mai taimakawa Gwamna a kafofin sadarwa na zamani, Isah Miqdad ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Facebook a yammacin Litinin.

Isah Miqdad ya ce Abdullahi Garba Faskari ne zai canji Arch. Ahmed Musa Dangiwa wanda zai zama Minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan Katsina
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, Ph.D. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Tsakanin 2011 da 2015, Faskari ne Mataimakin Gwamnan Katsina a mulkin Ibrahim Shehu Shema.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Yi Kamari, Tinubu Ya Zauna da Gwamnonin da ke Iyaka da Jamhuriyyar Nijar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a banza aka dawo da shi ba

Mutane da-dama sun yi mamakin jin yadda tsohon Mataimakin Gwamna wanda shi ne na biyu a jiha na tsawon shekaru hudu, zai zama sakatare.

Daga makwabta, Salihu Tanko Yakasai wanda ya yi takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2023, ya na cikin wadanda wannan nadi ya ba mamaki.

Amma Hadimin Gwamnan na Katsina ya nuna Faskari ya taba zama Kwamishinan ilmi, sannan ya rike kujerar babban Lauyan gwamnatin Jihar.

A cewar Miqdad, sabon Sakataren gwamnatin mutum ne da ya kware a fannoni dabam-dabam na shugabanci kuma za a ci moriyar sanin aikinsa.

Jama'a sun yi mamakin mukamin

Wani Bawan Allah ya ce babu dalilin sukar wannan nadi da aka yi domin an ga yadda mai neman takarar Gwamna ya kare da kujerar Kwamishina.

Kara karanta wannan

An Taso Tinubu, Ana Neman a Cire Tsohon Gwamna Daga Ministoci Kamar Shetty

Mahmud Jimoh ya ce:

"Mataimakin Gwamna ya zama Sakataren Gwamnatin Jiha? Tamkar Mataimakin Shugaban kasa ne ya dawo Sakataren Gwamnatin tarayya a matakin kasa."

Shi kuma wani Bishof Bishop Ifeanyi Emerald Ounah ya ce:

"‘Yan siyasa ba su da kunya Wallahi. Mataimakin Gwamna ya kare a SSG?"

Salihu Umar cewa ya yi: “Ban gane ba”

“Harkar nan ba wani cigaba ko ci baya in dai maiko ba zai tsaya ba.”

Inji Dr. Mohammed Alhaji.

“Allah SWT ya sa ya zama alheri ga al’umma jihar Katsina.”

- Aminu Ajiya

Legit.ng Hausa ta na sane da Abubakar Yahaya Kusada, wanda ya na cikin wadanda aka yi tunani za su iya samun mukamin, ya yabi Gwamnan.

Nadin mukami 62 a rana 1

Rahoto ya zo cewa Abba Kabir Yusuf ya nada mukamai da-dama a farkon makon nan. Mai girma Gwamnan jawo matasa cikin gwamnatin jihar Kano.

Wani ‘danuwan Rabiu Musa Kwankwaso ya samu mukami sannan Tijjani Gwandu, Oscar 442, Abba Dala da Sani Igwe duka sun shiga sahun hadimai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Janye Maryam Shetty, Ya Maye Gurbinta Da Mariya Daga Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel