Gwamnan Jihar Katsina Ya Raba N20m Ga Iyalan Yan Sakai Da Suka Rasa Ransu

Gwamnan Jihar Katsina Ya Raba N20m Ga Iyalan Yan Sakai Da Suka Rasa Ransu

  • Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya raba naira miliyan 20 ga iyalan ƴan sakai 33 da suka rasa ransu a jihar
  • Gwamnan ya bayyana rabon kuɗin a matsayin wani ɓangare na cika alƙawarin da ya ɗauka na yabawa da ayyukan masu samar da tsaro a jihar
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta raba naira miliyan 20 ga iyalai 33 na ƴan sakai waɗanda suka rasa ransu a bakin aiki.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan a wajen rabon kuɗin ga iyalan ƴan sakan da lamarin ya ritsa da su a birnin Katsina, ranar Asabar, 2 ga watan Satumban 2023, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Ɓullo da Sabon Tsari, Zai Gina Abu 1 a Kowace Gunduma a Najeriya

Gwamnan Katsina ya raba N20m ga iyalan yan sakai
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Radda wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Faskari, ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda za su amfana da tallafin, za su samu tsabar kuɗi har N500,000.

Gwamnan ya ƙara da cewa ƴan sakai 10 da suka samu raunika za su samu N250,000 kowannensu, yayin da iyalan wani jami'in soja da ya rasa ransa za su samu tsabar kuɗi naira miliyan ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da suka samu raunika a yayin hare-haren da aka kai kwanan nan, za a duba su nan ba da daɗewa ba.

Dalilin gwamna Dikko na raba N20m

Radda ya yi bayanin cewa wannan rabon kuɗin da ya yi na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe na yabawa da waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu da jindaɗinsu wajen kare jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fusata Kan Matsalar Tsaro, Zai Fallasa Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin 'Yan Ta'adda

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take wajen daƙile matsalar rashin tsaro da sauran laifuka a jihar.

"Ofishina a shirye ya ke ya karɓi shawarwari waɗanda za su taimaki gwamnatinmu wajen cika alƙawuran da ta ɗauka." A cewarsa.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗaga cikin ƴan kwamitin tsaro na ƙaramar hukumar Jibia, Malam Nasiru, wanda ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da gwamnan ya yi.

Malam Nasiru ya bayyana cewa wannan abun a yaba ne domin zai ƙara ƙarfin gwiwa ga dukkanin masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro, domin sun san cewa ko da ta Allah ta kasance, za a kula musu da abin da suka bari.

"Tabbas wannan abun a yaba ne domin ko ba daɗi an fitar da magada daga cikin yanayin da suka shiga." A cewarsa.

Gwamna Bago Ya Aike Da Sabon Gargadi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ja kunnun masu shirin karkatar da kayan tallafin da za a raba a jihar.

Gwamna Bago ya bayyana cewa duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan tallafin sai ya yi zaman gidan kaso komai girman muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng