Shugaban APC A Kano, Abbas Ya Jagoranci Murnar Cin Nasarar Zabe A Kotu

Shugaban APC A Kano, Abbas Ya Jagoranci Murnar Cin Nasarar Zabe A Kotu

  • Yayin da ake ci gaba da murnar kwace kujerar Gwamna Abba Kabir, Shugaban APC a jihar ya fita murna
  • An gano Abdullahi Abbas ya na saman mota inda ya ke tafi yayin da magoya bayan jam'iyyar APC su ke masa wake
  • Wannan na zuwa ne bayan kotu ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin gwamna

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya jagoranci murnar yin nasara a kotun zaben jihar.

Daruruwan matasa sun cika birnin Kano su na buga ganguna da wake-wake na goyon bayan tsohon Gwamna, Nasiru Gawuna.

Shugaban APC a Kano ya jagoranci murnar nasarar zabe
Shugaban APC A Kano, Abbas Abdullahi Ya Fita Murnan Samun Nasara. Hoto: Abbas Abdullahi.
Asali: UGC

Meye ya jawo murnar na magoya bayan APC a Kano?

Yayin gudanar da murnar, an gano Abbas na saman mota ya na tafi inda magoya bayan ke yabonsa a harshen Hausa, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An jiyo matasan na cewa:

"Allah ya kare Kano, Gawuna na zuwa, Nasara tamu ce."

Kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

Kotun ta kuma tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar a zaben da aka yi a watan Maris.

Kotun ta rusa nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben da aka gudanar a watan Maris na farkon wannan shekara.

Yadda Gawuna ya yi nasara a kotun zabe

Nasiru Gawuna wanda dan jam'iyyar APC ne kuma tsohon gwamnan jihar ya kalubalanci sahihancin zaben inda ya ke zargin an tafka magudi.

Kotun ta tabbatar da cewa akwai kuri'u fiye da dubu 165 da ba a saka musu hannu ba kamar yadda doka ta tanadar, Newnow ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Aike da Sako Ga Abba Gida-Gida Kan Tsige Shi da Kotun Zabe Ta Yi

Hakan ya sabawa dokar zabe wanda kotun ta ce kuri'un haramtattu ne yadda bai kamata a kirga su a cikin masu kyau ba.

A bangarenta, NNPP ta ce za ta daukaka kara kan wannan hukunci da aka yanke a yau Laraba.

Kotu ta tsige Abba Kabir na Kano, ta bai wa Gawuna kujerar gwamna

A wani labarin, a yau Laraba 20 ga watan Satumba, kotun sauraran kararrakin zabe ta kwace kujerar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a birnin Kano.

Har ila yau, kotun ta tabbatarwa Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC kujerar bayan gabatar da shaidu masu inganci.

Ana ci gaba da zaman dar-dar a birnin Kano tun bayan hukuncin kotun musamman tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel