Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC Nasara

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC Nasara

  • Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zabe ta bayyana hukuncinta dangane da ƙarar zaben gwamnan jihar Kano na ranar 18 ga watan Maris, 2023
  • A ranar Laraba, Kotun ta tsige Abba Gida-Gida kana ta ayyana Gawuna na APC a matsayin halastaccen zabaɓɓen gwamnan Kano
  • Wani jigon NNPP ya shaida wa Legit Hausa cewa sun san waɗanda suka yi ruwa suka yi tsaki aka yanke wannan hukuncin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Abba Ƙabir Yusuf daga kujerar gwamna, ta ayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben 18 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Yusuf, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Nasir Gawuna da Abba Kabir Yusuf.
Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC Nasara Hoto: Dr. Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yayin da Nasir Gawuna, babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC ya taya shi murna, jam’iyyar ta ce sam bata yarda ba, ta garzaya kotu, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gawuna Ya Yi Magana Kan Nasarar Da Ya Samu a Kotu, Ya Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf

Abinda ya sa Ƙotu ta tsige Abba Gida-Gida

Da take yanke hukunci ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, 2023, Kotun ta umarci INEC ta janye satifiket ɗin shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba na jam'iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma ta buƙaci INEC ta baiwa Nasir Gawuna na jam'iyyar APC Satifiket a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

Kotun ta zabtare ƙuri'u 165,663 daga cikin ƙuri'un da Abba ya samu a zaben da ya gabata saboda ba halastattu bane.

Ta bayyana cewa babu sutanfi ko sanya hannu a takardun ƙaɗa kuri'a guda 165,663, saboda haka Kotu ta bayyana su a matsayin haramtattu.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton cewa alkalan Kotu ba su halarci zaman yanke hukuncin ba, sun karanto hukuncin ne kai tsaye ta manhajar Zoom.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Ganduje, Gawuna Suka Yi Murna Bayan Kotu Ta Tsige Abba Ya Yadu

A halin yanzu dai, 'yan kasuwa da dama a manyan kasuwannin Kano sun kulle shagunansu sun koma gida domin gudun tashin hankalin da ka iya biyo baya.

Legit Hausa ta tuntuɓi wani jigon NNPP a Kano, Malam Saidu Abdu, kan wannan hukunci da Kotu da yanke, ya ce har yanzu suna da sauran damar tabbatar da nasarar Abba.

Ya ce duk da hukuncin bai musu daɗi ba, amma zasu ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da nasarar mai girma gwamna har zuwa Kotun koli idan da yiwuwar hakan.

"Abu bai mana daɗi ba kuma koma menene ya faru munsan haka Allah ya ƙaddara, amma muna da misalin abinda ya faru da gwamna Adeleke na Osun, zamu tafi Kotun ɗaukaka ƙara."
"Har kotun koli zamu je idan da yiwuwar hakan, ita dai Kotun zaɓe ta yi nata, ni dai ina zargin wasu masu son kai ne suka sa baki aka yi wannan hukuncin, ƙuri'un da aka soke ban san ina aka samo su ba."

Kara karanta wannan

"Akwai Kura-Kurai": Gwamna Abba Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu, Ya Bayyana Mataki Na Gaba Da Zai Dauka

Ondo: Sanatan APC Ya Nada Sabbin Hadimai 100, Zai Kowane Mutum Tallafin N300,000

A wani rahoton na daban kuma Sanatan Ondo ta kudu ya naɗa sabbin masu taimaka masa na musamman 100 'yan asalin mazaɓarsa.

Dakta Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa kowane ɗaya daga cikin waɗan nan mutane zai samu tallafin N300,000 a karon farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel