Dattawan Arewa Sun Yabawa Tinubu Kan Nadin Hakeem Baba-Ahmed Saboda Kwarewarsa

Dattawan Arewa Sun Yabawa Tinubu Kan Nadin Hakeem Baba-Ahmed Saboda Kwarewarsa

  • A karshe Kungiyar Dattawan Arewa, NEF ta yi martani kan mukamin da aka nada Dakta Hakeem Baba-Ahmed
  • Kungiyar ta ce tabbas nadin Dakta Hakeem ya nuna himmatuwar gwamnatin Shugaba Tinubu na kawo sauyi a kasar
  • Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya Talata 19 ga watan Satumba a Abuja a cikin wata sanarwa da Farfesa D. D Shehi ya fitar

FCT, Abuja – Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta tabbatar da samun labarin nada daraktan yada labaranta, Dakta Hakeem Baba-Ahmed.

Kungiyar ta ce nada Baba-Ahmed a matsayin mai ba da shawara ta bangaren siyasa da Tinubu ya yi abin a yaba ne.

Dattawan Arewa sun yabi Tinubu kan nadin Hakeem mukami
Dattawan Arewa Sun Yi Martani Kan Nadin Hakeem Baba-Ahmed Da Tinubu Ya Yi. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed.
Asali: Facebook

Meye Dattawan Arewa ke cewa kan Tinubu?

NEF ta bayyana haka ne a jiya Talata 19 ga watan Satumba a Abuja a cikin wata sanarwa da babban daraktan kungiyar, Farfesa D. D Shehi ya fitar, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kiristoci Sun Yi Amai Sun Lashe Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Sun Yabi Tinubu Kan Mukamai

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar ta taya Dakta Hakeem murnan samun wannan mukami inda ta ce tabbas hakan ya nuna himmatuwar gwamnatin Tinubu na dauko kwararru don kawo ci gaba a kasar.

Sanarwar ta ce:

“Kungiyar ta dauki wannan mukami na Shugaba Tinubu a matsayin hobbasa na nada kwararru don ciyar da kasar Najeriya gaba.”

Wani shawara Dattawan Arewa su ka bai wa Tinubu?

Ta kuma yi fatan Shugaba Tinubu zai yi amfani da kwarewar Dakta Hakeem wurin tabbatar da gyara a bangaren gudanarwa na kasar.

Shugaba Tinubu ya nada kakakin kungiyar a matsayin mai ba da shawara na musamman a bangaren siyasa ga mataimakinsa, Kashim Shettima.

Hakeem Baba-Ahmed ya kasance yaya ga Datti Baba-Ahmed wanda mataimaki ne ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Nadin Mukamai

Hakeem ya dade ya na sukar tsare-tsaren jam’iyyar APC mai mulki tsawon shekaru tun bayan hawan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tinubu ya nada Hakeem Baba-Ahmed babban mukami

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed matsayin hadimin Kashim Shettima a bangaren siyasa.

Hakeem ya kasance yaya ga Datti Baba-Ahmed, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyar Labour, Peter Obi.

Wannan mukami na Hakeem ya jawo cece-kuce ganin yadda ya ke sukar jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel