Kungiyar Kiristoci Ta Ce Yanzu Tinubu Ya Cire Musu Tsoron Tikitin Musulmi Da Musulmi

Kungiyar Kiristoci Ta Ce Yanzu Tinubu Ya Cire Musu Tsoron Tikitin Musulmi Da Musulmi

  • Kungiyar Matasan Kiristoci sun yabi yadda Shugaba Bola Tinubu ke nada mukamai ba tare da nuna wariya ga Kiristoci ba a kasar
  • Kungiyar ta ce a farko sun tsorata da tikitin Musulmi da Musulmi a lokacin yakin neman zabe amma yanzu Tinubu ya cire musu tsoro
  • Ta yabi Tinubu da nadin Kiristoci a manya-manyan mukamai kamar Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Kungiyar Kiristoci Matasa a Arewacin Najeriya (ACYNN) ta yabi Shugaba Tinubu kan yadda ya ke gudanar da gwamnatin ba warayya.

Kungiyar ta ce da farko ta yi tunanin tikitin Musulmi da Musulmi zai kawo matsala a kasar amma yanzu sun fahimci akwai adalci.

Kiristoci sun yaba wa Tinubu kan nadin mukamai
Kungiyar Kiristoci Ta Yi Martani Kan Nade-naden Mukamai Na Tinubu. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Kiristoci ke cewa kan mukaman Tinubu?

Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya Litinin 18 ga watan Satumba a Abuja yayin rangadin goyon baya ga gwamnatin Tinubu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Nadin Mukamai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kungiyar, Dominic Alancha ya ce da farko sun tsorata da tikitin amma daga baya sun fahimci akwai daidaito daga nade-naden gwamnati.

Ya ce:

“Da farko mun ki amincewa da tikitin Musulmi da Musulmi inda mu ke tunanini ba a dauke mu ‘yan kasa ba kwata-kwata.
“Amma yadda Shugaba Tinubu ya ke nada mukamai ya ba mu mamaki inda ya nuna adalci ga ‘yan Najeriya.”

Wani yabo Kiristocin su ka yi wa Tinubu?

Kungiyar ta yabi Tinubu na musamman kan nadin Kiristoci manya-manyan mukamai kamar Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da kuma hafsan tsaron kasar, Christopher Musa.

Ta bayyana nade-naden Tinubu da cewa babu wani wariya da son kai a yanayin yadda siyasar Najeriya ke tafiya da ta kunshi kowa da kowa.

Kiristocin sun roki ‘yan Najeriya da su bai wa Shugaba Tinubu da gwamnatinsa duk wani goyon baya don ciyar da kasar gaba, Allmedia News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu ya nada sabbin ministoci, an fadi sunaye da ma'aikatarsu

Sun kuma roki yin addu’o’I ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kuma mataimakinsa, Kashim Shettima don samun karin lafiya da kuzari don kawo ayyukan ci gaba a kasar.

MURIC ta soki Adeleke kan nada Kiristoci mukamai

A wani labara, kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta caccaki jerin sunayen kwamishinonin da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya fitar.

Majalisar Dokokin jihar Osun, ta karbi jerin sunayen wadanda Gwamna Adeleke ke son nadawa kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel